‘Yan Sanda sun damke Matashi dumu-dumu dauke da danyen kwarangal da hannuwan mutum

‘Yan Sanda sun damke Matashi dumu-dumu dauke da danyen kwarangal da hannuwan mutum

- ‘Yan Sanda sun kama wani mutumi dauke da kwakwalwar ‘Dan Adam a jaka

- Rundunar ‘Yan Sandan Kwara ta ce ana zargin wannan matashin matsafi ne

- Za a gurfanar da wannan mutum mai suna Kehinde John Moses gaban Alkali

Jami’an ‘yan sandan Najeriya na reshen jihar Kwara sun yi ram da wani matashi mai suna Kehinde John Moses da ake zargin matsafi ne.

A ranar Laraba, 5 ga watan Afrilu, Daily Trust ta rahoto cewa jami’an tsaron sun kama Kehinde John Moses ne dauke da danyen kan mutum.

Jaridar ta ce an kama wannan matashi mai shekara 24 da haihuwa ne a titin Ajase-Ipo/Ilorin, a lokacin da ‘yan sanda su ke binciken motoci.

KU KARANTA: Abin da ya hana a cafke Gumi - Tsohon Shugaban DSS

Da aka binciki jakar da wannan Bawan Allah yake dauke da ita, sai aka samu danyen kan mutum, da hannuwa da wasu bangarorin ‘Dan Adam.

Babban jami’in ‘yan sanda, Ajayi Okasanmi ya bayyana cewa Dakarunsu na Operation Harmony ne su ka yi nasarar kama Kehinde John Moses.

SP Ajayi Okasanmi ya ce da aka tasa Kehinde John Moses a gaba, ya amsa cewa ya kashe wani mutumi mai suna Mohammed a garin Ajase Ipo.

Wannan mutumi da ake zargi ya tabbatar da cewa sun yi amfani da Mohammed ne domin yin tsafi.

KU KARANTA: ‘Yan bindiga sun yi garkuwa da Shugaban Miyetti Allah da karfi da yaji

‘Yan Sanda sun damke Matashi dumu-dumu dauke da danyen kwarangal da hannuwan mutum
Kehinde John Moses Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

“Mun dauki masu bincike zuwa inda ya jefar da gawar wadanda aka kashe domin ayi tsafi, mun dauki gawar mun kai su asibiti.” Inji Okasanmi.

Mai magana da yawun bakin dakarun ‘yan sandan Kwara, Ajayi Okasanmi, ya bayyana cewa su na cigaba da gudanar da bincike a kan lamarin.

Da zarar ‘yan sanda sun karkare bincikensu, za a gurfanar da wannan mutumi zuwa gaban kotu.

A yau ne aka ji hukumar NDLEA ta yi nasarar kama wata tsohuwa dake sayar da miyagun kwayoyi, an kama wannan tsohuwa tare da jikarta.

Wata sanarwa daga kakakin NDLEA, Femi Babafemi, ya fitar a yau, ta bayyana cewa an cafke wadanda ake zargin ne bayan an samu bayanan sirri.

Asali: Legit.ng

Online view pixel