Jerin kasashe 20 mafi shugabannin kwarai a duniya, Rahoton Bincike

Jerin kasashe 20 mafi shugabannin kwarai a duniya, Rahoton Bincike

- Wata kungiyar shugabancin kwarai ta saki rahoto da ya nuna jerin kasashen duniya mafi shugabannin kwarai duniya

- A rahoto da kungiyar CGGI ta saki, kasar Finland ce kasa mafi shugabannin kwarai a duniya

- Babu kasar Afrika ko guda daya a cikin kasashen 20 na farko

Wata kungiya mai zaman kanta a kasar Singapore, Chandler Good Government Index, CGGI ta bayyana jerin kasashen da suka fi shugabannin kwarai a fadin duniya.

Rahoton da aka saki ranar 26 ga Afrilu, ya bayyana cewa an yi amfani da karfin iya yaki da rashawa wajen nuna irin nagartan shugabannin kasa.

CGGI ta saki rahotonta a shafinta na Tuwita.

Diraktan CGGI, Wu Wei Neng, ya ce mulki na kwarai ne abinda zai iya kawo wa kasa nasara.

Kara karanta wannan

Su suka bata Najeriya: Tinubu ya caccaki Atiku, ya ce PDP ba za ta lashe zaben 2023 ba

Ga jerin kasashen:

1. Kasar Finland

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

2. Kasar Swizalan

3. Kasar Singapore

4. Kasar Holland

5. Kasar Denmark

6. Kasar Norway

7. Kasar Jamus

8. Kasar Nuzilan

9. Kasar Kanada

10. Kasar Ireland

11. Kasar Birtaniya

12. Kasar Austria

13. Kasar Yaban

14. Kasar Estonia

15. Kasar Estonia

16. Kasar Australia

16. Kasar Faransa

18. Kasar Amurka

19. Kasar Iceland

20. Kasar Belguim

DUBA NAN:Gwamna El-Rufai ya bayyana dalilin yin amai ya lashe a kan masu garkuwa da mutane

Jerin kasashe 20 mafi shugabannin kwarai a duniya, Rahoton Bincike
Jerin kasashe 20 mafi shugabannin kwarai a duniya, Rahoton Bincike Credit: @ChandlerINST
Asali: Twitter

DUBA NAN: Sanatoci sun shiga dimuwa, sun ce da yiwuwan yan Boko Haram su kai hari Abuja

A bangare guda, CGGI ta bayyana Najeriya a matsayin kasa maras shugabannin kwarai ta uku a fadin duniya.

Rahoton ta baiwa Najeriya maki mai rauni wajen mulkin kwarai, inda Najeriya ta zo na 102 cikin kasashe 140 da maki 0.319.

Kara karanta wannan

Karin bayani: APC ta kaddamar da tawagar mata da za su tallata Tinubu gabanin 2023

Kasashen da Najeriya tafi shugabannin kwarai a cewa rahoton Zimbabwe da Venezuela ne kadai.

Asali: Legit.ng

Authors:
AbdulRahman Rashida avatar

AbdulRahman Rashida