Abin da APC za ta yi idan ta na sha'awar ta cigaba da mulkin kasar nan – Jigon Jam’iyya

Abin da APC za ta yi idan ta na sha'awar ta cigaba da mulkin kasar nan – Jigon Jam’iyya

- Honarabul Aminu Sani Jaji ba ya goyon bayan tsarin kama-kama a siyasa

- ‘Dan siyasar ya na ganin duk mai sha’awar shiga takara, ya fito a gwabza

- Tsohon ‘Dan Majalisar ya ce su na maraba da zuwan Bello Matawalle APC

Aminu Sani Jaji, tsohon ‘dan majalisar tarayya daga jihar Zamfara, ya yi hira da Daily Trust, inda ya tabo batutuwa da-dama, daga ciki har da zaben 2023.

A hirar da aka yi da Honarabul Aminu Sani Jaji, ya ba gwamnati shawarar yadda za ta yi maganin matsalar rashin tsaro da yadda APC za ta zarce.

Da aka tambayi Aminu Jaji game da rade-radin sauya-shekar gwamnan Zamfara, Bello Matawalle daga jam’iyyar PDP, ya ce su na maraba da shi cikin APC.

KU KARANTA: Yadda Jonathan ya nemi ya daure ni - El-Rufai

“Mu na maraba da shigowar gama-gari ma, ina ga gwamna mai-ci? Ba mu da damar hana shi sauya-sheka, idan ya na sha’awa, sai ya shigo.” Inji Jaji.

Tsohon ‘dan majalisar ya ce zuwan Bello Matawalle APC bai nufin zai samu tikitin takarar tazarce a 2023, ya ce sai abin da manyan jam’iyya su ka shirya.

Jaji ya tabbatar da mubaya’arsa ga tsohon gwamna Abdulaziz Yari, ya ce shi ne jagoran APC a Zamfara, kuma akwai wasu masu harin kujerar gwamna.

Game da kama-kama da ake yi wajen neman takara, Jaji ya ce ba ya goyon-bayan wannan tsari, ya ce duk mai neman wata kujera ya fito ayi takara da shi.

KU KARANTA: NUJ za ta ba Shugaban majalisa, Sanata Barau kyautar lambar yabo

Abin da APC za ta yi idan ta na sha'awar ta cigaba da mulkin kasar nan – Jigon Jam’iyya
Hon. Hon. Aminu Sani Jaji Hoto: www.dailytrust.com
Asali: UGC

“Ni sam ba na goyon bayan wannan. Duk wani da yake ganin ya isa ya yi takarar shugaban kasa, ya fito ya nemi kuri’u, ba ‘yan jam’iyya ne kurum su ke zabe ba.”

Ya ce: “Duk mai neman zama shugaban kasa, ‘dan siyasa ne shi, ya zagaye jihohi 36 da birnin tarayya Abuja, idan mutane sun yi na’am da shi, su zabe shi.”

Dazu kun ji cewa Olusegun Obasanjo ya na sha’awar Shugaban AfDB, Akinwumi Adesina ya samu takarar kujerar shugaban kasa a 2023 bayan an samu rikici a PDP.

Mun fahimci cewa Olusegun Obasanjo ba ya goyon bayan takarar Bola Tinubu, ya na tare da Dr. Adesina wanda ya rike Ministan harkar gona a Gwamnatin PDP.

Asali: Legit.ng

Online view pixel