Tsohon Shugaban kasa Obasanjo ya bayyana matsayarsa a kan kiraye-kirayen raba Najeriya

Tsohon Shugaban kasa Obasanjo ya bayyana matsayarsa a kan kiraye-kirayen raba Najeriya

- Olusegun Obasanjo ya ce dole a 2023 ayi wa Najeriya sabon lale ko a samu matsala

- Tsohon Shugaban ya ce kasar nan za ta iya wargaje gaba daya idan har aka yi sake

- Obasanjo ya ce kananan kabilu sun fi samun kariya yayin da Najeriya ke a dunkule

Tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo, ya bayyana cewa akwai bukatar shugabanni su tabbatar da Najeriya ta dauki sabuwar alkibla.

A ranar Larabar nan ne, tsohon shugaban Najeriyar ya yi gargadi cewa muddin abubuwa ba su sake zani a 2023 ba, kasar nan za ta zama tarihi.

Olusegun Obasanjo ya yi wannan bayani ne a garin Abeokutan jihar Ogun, yayin da ya karbi bakuncin wata kungiya ta masanan kabilar Tiv.

KU KARANTA: Za a dauke Almajirai 7, 000 daga Katsina, a maida su gidajen Iyayensu

Shugaban wannan kungiya TPG, Farfesa Zacharys Anger Gundu ya jagoranci mutanensa zuwa wajen Obasanjo wanda ya yi mulki har sau biyu.

Obasanjo ya ce dole ne shekarar 2023 ta zo da sabo salo domin a samu zaman lafiya a Najeriya. Jaridar Daily Trust ta fitar da wannan rahoto dazu..

Ya ce: “Na yarda ayi duk abin da za ayi domin ganin 2023 ta zo da wani salon albarka ga Najeriya. Dole 2023 ta ba mu alkiblar kafa sabuwar kasa.”

“Idan ba ayi wannan ba, za mu cigaba da fama da matsalar da ake fuskanta, daga nan sai kuma kasar ta wargaje gaba daya.” Inji Olusegun Obasanjo.

KU KARANTA: Shugabannin kasar nan da su ka mutu a kan karagar mulki

Tsohon Shugaban kasa Obasanjo ya bayyana matsayarsa a kan kiraye-kirayen raba Najeriya
Tsohon Shugaban kasa Janar Olusegun Obasanjo Hoto: www.thisdaylive.com
Asali: Twitter

A cewar Obasanjo, masu buga gangar rabuwar kan al’umma, ba su yin la’akari da sauran kananan kabilu marasa rinjaye da ake da su a kasar nan.

Idan Yarbawa, Ibo da Hausa su ka balle daga Najeriya, suka kafa kasar kansu, Obasanjo ya ce babu inda za a kai sauran kabilun da ba su da yawa.

“Abin da mutane basu sani ba kenan. Ina za a jefa kananan kabilu? Idan aka barka kasar nan, za a rika gallaza masu sosai. Muna tunanin wannan?

Kwanaki aka ji tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo ya goyi bayan Sheikh Ahmad Abubakar Gumi a kan batun yafe wa miyagun 'yan bindiga

Olusegun Obasanjo ya bada shawara ga gwamnatin Muhammadu Buhari ta yi afuwa ga tubabbun 'yan bindiga da suka shirya yin tuba, su bar daji.

Asali: Legit.ng

Online view pixel