Gwamnatin Jihar Katsina ta fara maida Almajirai 7, 000 zuwa asalin Garuruwan da su ka fito

Gwamnatin Jihar Katsina ta fara maida Almajirai 7, 000 zuwa asalin Garuruwan da su ka fito

- Gwamnatin jihar Katsina ta fara maida Almajiran ta zuwa ainihin kauyukansu

- Hussaini Adamu-Karadua ya ce sun gano Almajirai 7, 000 da su ka zo daga waje

- A jiya ne Hasfat Muhammad-Baba ta karbi Almajiran da su ka fito daga jihar Kaduna

Jaridar Katsina Post ta fitar da cewa gwamnatin jihar Katsina ta soma maida wasu Almajiran makarantun allo zuwa ainihin jihohin da su ka fito.

Rahotanni sun tabbatar da mana cewa yara 7, 054 da su ke karantun allo a jihar Katsina aka dauke, ana maida su garuruwan da iyayensu su ke.

Shugaban kwamitin da ke tara alkaluman almajirai na jihar Katsina, Malam Hussaini Adamu-Karadua, ya bayyana wa manema labarai wannan.

KU KARANTA: Gwamnatin Kaduna ta ce ta ceto kananan Almajirai 160

Da yake magana da ‘yan jarida ranar Laraba a garin Funtua, Hussaini Adamu-Karadua, ya bayyana haka.

Adamu-Karadua ya bada wannan sanarwa ne yayin da yake mika wa jami’an gwamnatin Kaduna wasu daga cikin daliban da su ka fito daga jihar.

Shugaban wannan kwamiti ya tabbatar da cewa duka gwamnonin jihohin Arewa 19 sun goyi bayan wannan matakin da gwamnatin Katsina ta dauka.

Jami'in ya ce: “Kwamitin ya gano Almajirai 7, 054 da su ka fito daga wasu wuraren, su na koyon karatun Al-Qur’ani a wurare da-dama a cikin jihar Katsina.”

KU KARANTA: Rabuwa da Uwar ‘Ya ‘yansa ta sa Bill Gates zai rasa Biliyoyin kudi

Gwamnatin Jihar Katsina ta fara maida Almajirai 7, 000 zuwa asalin Garuruwan da su ka fito
Gwamnan Jihar Katsina Hoto: www.bbc.com/hausa/labarai-49650599
Asali: UGC

Ya ce: “Za a maida su jihohin da su ka fito daya-bayan-daya, za mu kawo dabarun da za su taimaka mana wajen cin ma wannan buri da mu ka dauka.”

Shugaban kwamitin ya ce dalibai kusan 2, 000 sun fito ne daga kasar Jamhuriyyar Nijar, yayin da sauran su ka shigo Katsina daga wasu jihohin da ke Najeriya.

A na ta bangaren, gwamnatin Kaduna ta bakin Kwamishinar cigaba da walwalar jama’a, Hasfat Muhammad-Baba, ta yabi kokarin da gwamnatin Katsina ta yi.

Muhammad-Baba ta ji dadin yadda gwamnatin jihar Katsina ta dauki dawainiyar Almajiran.

Asali: Legit.ng

Online view pixel