Rawar da mahaifin kasurgumin dan bindiga ya taka wajen kubutar daliban Afaka 27

Rawar da mahaifin kasurgumin dan bindiga ya taka wajen kubutar daliban Afaka 27

- Daliban kwalejin FCFM Afaka sun samu kubuta bayan kimanin watanni biyu cikin daji

- An kai su hedkwatar yan sanda son duba lafiyarsu

- Mahaifin daya daga cikin yan bindiga ya sanya baki cikin lamarin kan a sakesu

Kwanaki 55 bayan sace dalibai daga makarantar fasahar gandun daji a Afaka, karamar hukumar Igabi ta jihar Kaduna, an saki sauran dalibai 27 dake hannun yan bindigan ranar Laraba.

Mun kawo muku yadda aka tarbi daliban a hedkwatar yan sandan da yammacin Laraba bayan an biya yan bindigan kudin fansa N15m tare da sakin wani kasurgumin dan bindiga.

Asali dalibai 38 yan bindigan suka sace daga makarantar amma daya ya samu kubuta.

Daga baya kuma yan bindigan suka saki 10 bayan biyansu kudin fansan sake dukkan daliban.

Tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo, da babban Malami Sheikh Ahmad Gumi sun taka rawar gani wajen samun yancin daliban.

A riwayar Daily Trust, akwai sauran mutum daya wanda ya taka rawar gani wajen tattaunawa da yan bindigan kuma mahaifin daya daga cikin tsagerun yan ta'addan ne.

KU KARANTA: Ba zamu taba yarda wani ya shigo da Masara daga waje ba, gwamnan CBN

Rawar da mahaifin kasurgumin dan bindiga ya taka wajen kubutar daliban Afaka 27
Rawar da mahaifin kasurgumin dan bindiga ya taka wajen kubutar daliban Afaka 27
Asali: Getty Images

KU DUBA: Muna hasashen za'ayi ambaliya a jihohi 28 bana, Ministan Ruwa ya lissafo su

A cewar majiyoyi, an samu cikas yayin tattaunawa bayan shugaban tsagerun, Baderu, ya saba alkawarinsa bayan biyasa kudin fansan N15m.

Amma mahaifin wani mai suna Buhari, wanda shima kasurgumin dan bindiga ne ya saka baki.

Majiyoyi sun bayyana cewa mahaifin ya yi amfani da 'dansa wajen tilasta Baderu cika alkawarinsa, amma Baderu yace ko da ba za'a kara kudi ba, sai an saki dan'uwansa da aka kama a dajin Falgore, jihar Kano.

Bayan sake 'dan uwan nasa wanda shima dan bindiga ne mai suna Laulu, sai aka saki daliban.

A bangare guda, Fusatattun matasa sun kashe wasu mutane uku da ake zargin masu garkuwa da mutane ne a yayin da suka yi yunkurin kai hari a Goronyo a ranar Laraba, Daily Trust ta ruwaito.

Matasan sun kuma ƙona ofishin ƴan banga da aka fara ajiye wadanda ake zargin.

Yan bindigan sun zo wani Rugar Fulani da ke wajen Goronyo cikin dare domin su sace shanu amma mutanen suka yi fito-na-fito da su suka kama uku cikinsu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel