Siyasar 2023: Ana kutun-kutun za a dakatar da Shugaban APC saboda hada-kai da Tinubu

Siyasar 2023: Ana kutun-kutun za a dakatar da Shugaban APC saboda hada-kai da Tinubu

- Akwai yiwuwar APC ta dakatar da wani shugaban jam’iyyar ta a garin Ado, Ekiti

- Ana zargin Clement Afolabi da yin alaka da kungiyar magoya bayan Bola Tinubu

- A halin yanzu akwai hamayya tsakanin ‘Yan Gwamna Fayemi da yaran Tinubu

Jam’iyyar APC a karamar hukumar Ado a Ekiti, ta fara shirin dakatar da shugaban rikon kwarya na wata mazaba saboda alakarsa da kungiyar SWAGA.

Jaridar Daily Trust ta fitar da rahoto cewa Clement Afolabi ya gamu da matsala ne a dalilin zargin da ake yi masa na hulda da wannan kungiya ta SWAGA.

Kungiyar South West Agenda ba ta taba boye muradunta na yi wa Bola Tinubu yakin neman zabe ba.

KU KARANTA: Magoya bayan Tinubu sun fadi yarjejeniyar da aka yi kafin 2015

Ana zargin Clement Afolabi wanda shi ne shugaban rikon-kwarya na mazabar Ado Ward 8 ya na tare da masu goyon bayan takarar Bola Tinubu a 2023.

Matakin da Afolabi ya dauka na bin jirgin tsohon gwamnan Legas, Asiwaju Bola Tinubu, ya fusata shugabanninsa na jihar Ekiti da ke tare da Kayode Fayemi.

Ana zargin shugabannin jam’iyyar APC na jihar Ekiti su na mara wa Kayode Fayemi baya ne domin ganin ya samu tikitin takarar kujerar shugaban kasa.

Mista Clement Afolabi ya fito ne daga yankin da babban mai ba shugaban kasa shawara a kan harkokin siyasa, Sanata Babafemi Ojudu, ya fito, a jihar Ekiti.

KU KARANTA: Ana rikici da Babafemi Ojudu a APC a jihar Ekiti

Siyasar 2023: Ana kutun-kutun za a dakatar da Shugaban APC saboda hada-kai da Tinubu
Gwamnan Ekiti, Kayode Fayemi

A shekarar bara ne Afolabi ya dakatar da hadimin shugaban kasar daga jam’iyyar APC saboda ya na yawan sukar gwamnatin mai girma Dr. Kayode Fayemi.

Bayan ya dakatar da tsohon Sanatan, sai aka ji manyan APC sun gayyace shi ya bayyana a gaban kwamitin ladabtar wa, inda ake zargin shi da laifin zagon-kasa.

A takardar, shugaban APC na karamar hukumar Ado, Temitope Oluwasola, ya ce ana zargin Afolabi da zama shugaban wata kungiya mara gindin zama.

A yau ne ku ka ji cewa Gwamnan jihar Oyo ya yi wa Bola Tinubu raddi na cewa za su cigaba da mulki, ya ce jam’iyyar APC ba za ta zarce 2023 a kan mulki ba.

Gwamna Makinde ya sha alwashin ganin Jam’iyyar PDP ta sake karbe mulkin kasa. Hakan na zuwa ne bayan Tinubu ya fito ya na cewa APC za ta zarce a 2023.

Asali: Legit.ng

Online view pixel