Wata sabuwa: Rikici ya sake barkewa a jam'iyyar APC a jihar Ekiti

Wata sabuwa: Rikici ya sake barkewa a jam'iyyar APC a jihar Ekiti

Rikicin jam’iyyar APC a jihar Ekiti ya dauki sabon salo a ranar Laraba bayan zargin yunkurin tsige mai bai wa shugaban kasa Muhammadu Buhari shawara a kan harkokin siyasa, Sanata Babafemi Ojudu ya tashi a tutar babu.

Shugabannin jam’iyyar da jami'an unguwa ta 8 na karamar hukumar Ado ekiti sun tsallake kwamitin gudanar da ayyuka na APC na jihar inda suka yi yunkurin dakatar da Ojudu a kan rashin biyayya.

Hadimin shugaban kasar da Gwamna Kayode Fayemi sun taba rikici bayan da hadimin shugaban kasar ya zargi gwamnan da rashin aiki tare da salon mulki na kama-karya a jam’iyyar.

Wata sabuwa: Rikici ya sake barkewa a jam'iyyar APC a jihar Ekiti
Wata sabuwa: Rikici ya sake barkewa a jam'iyyar APC a jihar Ekiti Hoto: Sahara Reporter
Asali: UGC

Baya ga ruwan kalamai masu zafi da ya shiga tsakaninsu, Ojudu tare da goyon bayan Dr Wole Oluyede, Oyetunde Ojo, Chief Akomolafe, Ayo Ajibade, Bunmi Ogunleye da Ben Oguntuase, a madadin fusatattun ‘yan jam’iyyar, sun kara garzayawa kotu.

A kotun sun kalubalanci shugaban jam’iyyar na unguwa, karamar hukuma da jiha ta yadda suka samu mulkin.

A makon da ya gabata, Ojudu ya zargi kwamitin gudanar da ayyuka na unguwa ta takwas da ke Ado Ekiti da amfani da umarnin Fayemi wajen fara yunkurin dakatar da shi.

Ya yi zargin cewa an yi garkuwa da shugaban APC na unguwar ta takwas, Clement Afolabi don tirsasa shi dakatar da Ojudu.

Amma kuma a maimakon dakatar da shi, kwamitin gudanar da ayyuka na jam’iyyar sai suka masa kuri’ar kwarin guiwa da tabbaci.

Kamar yadda shugabannnin jam’iyyar suka bayyana a taronsu na ranar Laraba, sun tabbatar da cewa Ojudu bai yi wani laifi da zai sa a dakatar da shi ba.

Sun bayyana shi a matsayin dan jam’iyya nagari mai bada gudumawa wajen habbakar jam’iyyar APC a kasar nan.

A wata takardar da Afolabi ya saka hannu sannan ya bai wa manema labarai, shugabannin jam’iyyar sun tabbatar da cewa babu wani tsoratarwa ko kuma kudi da za a basu da zai sa su dakatar da Ojudu.

Sun tabbatar da cewa karkon jam’iyyarsu ya rataya ne a wuyan ingantattun shugabanninsu.

KU KARANTA KUMA: Zaben Edo: Ban janye wa Obaseki ba - Dan takarar PDP

Kamar yadda yace, “Sanata Babafemi Ojudu dan asalin unguwa ta 8 ne kuma jakadenmu ne mai wakiltarmu. Yana da kokari tare da dagewa. Babu shakka mai ruwa da tsaki ne a jam’iyyarmu da yankinmu baki daya.

“Ojudu bai yi wani laifi ba da ya cancanci ladabtarwa. Ya nuna rasin gamsuwarsa ne da wasu al’amura na jam’iyyar.

“A don haka ne muka saka mishi kuri’ar kwarin guiwa a matsayinsa na dan jam’iyya mai biyayya.”

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel