Buhari ya lissafo mutum 3 da su ka bada gudumuwa wajen ceto ‘Daliban Kaduna

Buhari ya lissafo mutum 3 da su ka bada gudumuwa wajen ceto ‘Daliban Kaduna

- Muhammadu Buhari ya yi magana game da daliban da aka ceto a Kaduna

- Shugaban kasar ya yi farin cikin samun labarin kubuto da wadannan yaran

- Buhari ya yabawa kokarin da Jami’an tsaro da Gwamnatin Kaduna suka yi

Mai girma Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ji dadin sakin ‘daliban makarantar gandun daji ta Afaka a garin Kaduna da aka yi garkuwa da su.

Shugaban Najeriyar ya bayyana farin cikinsa a lokacin da yake magana game da ceto yaran makarantar.

Muhammadu Buhari ya bayyana wannan a wani jawabi da ya fitar a shafinsa na Twitter, a ranar 5 ga watan Mayu, 2021, bayan ‘yan makarantar sun fito.

KU KARANTA: Biyan kudin fansa ba haram ba ne - Gumi

Wadanda su ka yi garkuwa da daliban makarantar sun rike su na tsawon kwanaki fiye da 50. Sai a ranar Laraba ne aka yi dace, ‘yan bindiga su ka sake su.

Da yake magana, shugaban kasar ya gode wa abokai da ‘yanuwan wadannan Bayin Allah, sannan kuma ya yabi irin kokarin da gwamnatin jihar Kaduna tayi.

Gwamnatin Kaduna a karkashin Malam Nasir El-Rufai ba ta goyon bayan a yi sulhu da ‘yan bindiga, hakan ya sa ta haramta wa kan ta biyan kudin fansa.

Muhammadu Buhari ya gode da yadda na-kusa da wadannan yara su ka dafe da addu’a har su ka fito.

KU KARANTA: Ya kamata Pantami ya sauka daga mukaminsa - NATCOMS

A jawabin na sa a jiya, shugaban Najeriya ya ambaci jerin mutane da hukumomin da suka taka rawar gani wajen ganin ‘daliban makarantar sun dawo gidajensu.

1. Hukumomi da jami’an tsaro

2. Jami’an ma’aikatar muhalli.

3. Gwamnatin jihar Kaduna

Shugaban kasar yake cewa: "Mun yi farin ciki da aka fito da su."

Jiya ne fitaccen Malamin addini, mazaunin garin Kaduna, Ahmad Gumi ya musanta zarginsa da ake yi da hada iyayen daliban Afaka da wani da su ka ba kudi.

Gumi ya ce zargin da aka yi masa na hada su da wani mutum har ya karba musu N800,000 rashin hankali ne kuma sam bai san komai a kan wannan magana ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel