An Ƙona Gidan Wani da Ake Zargin Shugaban IPOB Ne a Imo

An Ƙona Gidan Wani da Ake Zargin Shugaban IPOB Ne a Imo

- Jami'an tsaro sun cinnawa gidan wani Moputu mai shekara 50 da ake zargin yana cikin shugabannin IPOB

- Jami'an yan sanda sun dauki tsawon lokaci suna bincike a gidan kafin daga bisani su kone gidan

- Mai magana da yawun yan sandan Jihar Imo ya ce bai samu labarin faruwar lamarin ba

An ruwaito cewa anyi harbe-harbe tare da kona wani gida a Umuneke-Nta a karamar hukumar Isiala Mbano da ke Jihar Imo bayan jami'an tsaro sun mamaye yankin da safiyar Talata, Daily Trust ta ruwaito.

An tabbatar da cewa jami'an tsaron sun shiga yankin don neman wani shugaban yan fafutukar kafa Biafra, Theddus Ekechukwu, mai shekaru 50, da aka fi sani da Moputu.

An Ƙona Gidan Wani da Ake Zargin Shugaban IPOB Ne a Imo
An Ƙona Gidan Wani da Ake Zargin Shugaban IPOB Ne a Imo. Hoto: @daily_trust
Asali: UGC

DUBA WANNAN: Rashin Tsaro: Gwamna Bagudu Ya Buƙaci Ƴan Nigeria Su Koma Ga Allah

Ekechukwu, wanda matarsa jami'ar yan sanda ce, an ganshi a unguwar har yammaci kafin faruwar lamarin.

Wani shaidar gani da ido ya ce jami'an tsaro sun shiga unguwar kimanin mota bakwai, ciki har da tankar yaki.

Shaidar ya ce jami'an tsaron sun saka kananan riguna an rubuta POLICE a baya. Kuma an rubuta 'FBI-R' a jikin motocinsu.

Majiyar ta ci gaba da cewa jami'an tsaron sun isa unguwar da misalin karfe 1:00 na dare tare da daura sarka a gidan Moputu a wani yunkurin kama shi.

"Amma bayan dogon bincike a gidansa, ba su same shi ba. Wasu sun ce ya gudu bayan ya fuskanci akwai matsala.

KU KARANTA: Jonathan Ya Yi Jinjina Ga Tsohon Mai Gidansa Ƴar’Adua Shekaru 11 Bayan Rasuwarsa

"Cikin bacin rai, da misalin 8:00 am, yan sandan sun cinna wuta a gidan a gaban iyalansa da yan uwansa.

"Wutar tayi barnar dukiyoyi da dama ciki har da babban inji, firji, sabon babur da ma wasu da dama.

"Amma sai dai, da yawa daga cikin kayan da suka kone ba na Moputu bane. Na yayansa ne wanda ya bashi matsuguni da shi da iyalansa.

"Bayan haka, sun ci gaba da harbi a iska lokacin da suke barin unguwar ta yankin Amaraku. Ba wanda abin ya shafa saboda ina tunanin iya Moputu suke nema."

Mai magana da yawun yan sanda, Orlando Ikeokwu ya ce bai samu labarin faruwar lamarin ba.

A wani labarin daban tsohon mataimakin shugaban kasa Mr Atiku Abubakar, a ranar Litinin, ya zargi gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari da musgunawa kafafen watsa labarai da yi wa yan kasa barazana idan sun bayyana ra'ayoyinsu.

Atiku ya yi wannan zargin ne cikin wani rubutu da ya wallafa a shafinsa na Twitter @atiku domin bikin ranar Yan Jarida na Duniya.

Ya bayyana cewa idan ana tauye hakkin mutane a mulkin demokradiyya, hakan zai kawo rashin jituwa tsakanin mutane da gwamnatin kasa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel