Kungiyar NUJ za ta karrama Kyari, Gbajabiamila, Sanatan Kano da wasu fitattu a bana

Kungiyar NUJ za ta karrama Kyari, Gbajabiamila, Sanatan Kano da wasu fitattu a bana

- Kungiyar NUJ ta shirya yadda za a gudanar da bikin ranar ‘yan jarida na bana

- NUJ za ta gudanar da wata laccar musamman domin tuna wa da wannan ranar

- Mele Kyari, Femi Gbajabiamila suna cikin wadanda za su iya samun lambar yabo

Kungiyar NUJ ta ‘yan jaridan Najeriya ta kammala shirye-shiryen karrama wasu mutane da kamfanoni saboda gudumuwar da su ka bada.

Jaridar This Day ta fitar da rahoto cewa kungiyar NUJ za ta ba gidan talabijin na Arise News lambar yabo na bada kariya ga hakkin ‘yan jarida.

Wadanda aka zaba a matsayin wadanda ‘yan jarida su ke jin dadin hulda da su sun hada da Nigeria Info FM, babban bankin CBN, da Access Bank.

KU KARANTA: Gwamnatin Buhari ta na musgunawa 'Yan jarida

Bayan laccar da za a shirya, kungiyar ‘yan jarida ta kasar za ta bada lambobin yabo ga wasu daidaiku.

Sanarwar da kungiyar ta fitar ta ce za a yi wannan bikin bada lambar yabo ne a ranar Laraba, 5 ga watan Mayu, 2021, a babban birnin tarayya Abuja.

Mataimakiyar sakatariyar kungiyar NUJ ta kasa, Midat Joseph, ta bayyana cewa za a gudanar da wata lacca ta musamman a bikin wannan shekarar.

Midat Joseph ta bayyana cewa daga cikin wadanda za a ba kyautar lambar yabo akwai shugaban majalisar wakilan tarayya, Rt. Hon. Femi Gbajabiamila.

KU KARANTA: Buhari ya na kaunar matasan Najeriya inji Gwamnan Kogi

Kungiyar NUJ za ta karrama Kyari, Gbajabiamila, Sanatan Kano da wasu fitattu a bana
An zabi CBN cikin wadanda za a iya ba kyauta Hoto: www.premiumtimesng.com
Source: Facebook

NUJ ta sa gwamnan Bayelsa, Sanata Douye Diri da shugaban kamfanin mai na NNPC na kasa, Mele Kolo Kyari a cikin wadanda za ta iya karrama wa.

Shugaban majalisar dokokin jihar Abia, Rt. Hon. Chinedum Orji ya na cikin wadanda aka zaba cikin wadanda za su lashe kyautar ‘Abokan ‘yan jarida’.

Haka zalika wadanda za su iya lashe lambar yabon masu kare ‘yan jarida su ne: James Ume; Sanata Jibrin Barau da kuma Dr. Samson Agada Omale,

Za a shirya wannan gagarumin biki ne domin tuna wa da ranar kare hakkin ‘yan jarida ta Duniya.

Kafin yanzu mun tattaro maku wasu tsofaffin Gwamnonin Jihohin da su ke da ta-cewa a Jihohinsu, shekaru aru bayan sun bar kan karagar mulki.

Shekara da shekaru an gagara dusar da hasken tauraruwar wadannan fitattun ‘Yan siyasa. Daga cikin su akwai Rabiu Kwankwaso da Asiwaju Bola Tinubu.

Source: Legit.ng

Online view pixel