2023: An gano wanda Tsohon Shugaban kasa Obasanjo ya ke goyon baya ya gaji Buhari
- Olusegun Obasanjo ya na sha’awar Dr. Akinwumi Adesina ya nemi Shugaban kasa
- Ya yi hakan ne bayan ya gaza shawo kan Rabiu Kwankwaso da Aminu Tambuwal
- Shugaban bankin AfdB, Dr. Akinwumi Adesina ya rike Minista a Gwamnatin PDP
Majiyoyi masu karfi na-kusa da Olusegun Obasanjo sun bayyana cewa tsohon shugaban kasar ya na yi wa Dr. Akinwumi Adesina harin kujerar shugaban kasa.
Reuben Abati ya rahoto cewa tsohon shugaban kasar Najeriyar ya na so Dr. Akinwumi Adesina ya shiga cikin masu neman takarar shugabancin Najeriya a 2023.
Hakan na zuwa ne bayan ya gagara shawo kan gwamna Aminu Tambuwal da Sanata Rabiu Kwankwaso su hada-kai domin kai jam’iyyar PDP ga nasara.
KU KARANTA: Rashin tsaro: Gwamnan APC ya bukaci a komawa Ubangiji
Na-kusa da tsohon shugaban kasar sun bayyana cewa Olusegun Obasanjo ya je Sokoto a makon da ya wuce ne domin ya sasanta gwamna Tambuwal da Kwankwaso.
“A makon jiya Baba ya je Sokoto da sunan kaddamar da wasu ayyukan da gwamnatin Tambuwal ta kammala, amma ainihin dalilin ziyarar ita ce ya sulhunta gwamna Aminu Tambuwal da Rabiu Kwankwaso.”
“Dukkansu (biyun) ‘ya ‘yansa ne a siyasa, kuma su na harin kujerar shugaban kasa.” Inji majiyar.
“Ta kuma bayyana karara cewa Baba ya na kokarin tado wani yaron na sa a jam’iyyar PDP, shi ne shugaban bankin cigaban Afrika, Dr. Akinwumi Adesina.”
KU KARANTA: Kwankwaso, Tinubu, da sauran tsofaffin Gwamnoni da su ke tashe har gobe
Majiyar ta ce Obasanjo ya dauki wannan matsaya ne ganin kan manyan Arewa ya ki hadu wa.
Wani ‘dan siyasa ya ce: “Baba ya na goyon bayan shugaban AfDB ne saboda ilmin bokonsa da tattalin arziki da kware wa a shugabanci, ya na ganin zai kai labari.”
Rahoton ya ce Obasanjo ya fara samun cikas domin tsofaffin shugaban kasar da aka kai wa wannan labari su na goyon bayan ‘yan kabilar Ibo da Bola Tinubu ne a 2023.
Jiya ne ku ka ji cewa Eidrez Abdulkarim ya shiryawa Festus Keyamo SAN, wakar gambara bayan sun samu sabani, inda har ta kai Ministan ya fito yana tona masa asiri.
Fallasa Fitaccen Mawakin a idanun Duniya ya jawo an yi wa karamin Ministan kwadago, Keyamo wakar cin mutunci. Har Dr. Isa Pantami ba a kyale a wakar ba.
Asali: Legit.ng