Babban Hasafi: Mai kudin Duniya, Jeff Bezos, ya saki Matarsa

Babban Hasafi: Mai kudin Duniya, Jeff Bezos, ya saki Matarsa

- Mai kamfanin hada-hadar kasuwanci na duniya Amazon, Jeff Bezos, ya saki Matar sa inda za ta hasafin rabuwa na N12.5 trn

- Jeff Bezos wanda ya fi kowa kudi a duniya na da tarin dukiya ta N53 trn inda ya auri Matar sa a shekarar 1993

- Ma'auratan bayan sun haifi 'ya'ya hudu sun amince da sawwakewa junan su tare a ci gaba da rike zumunci da kyakkyawar alaka a tsakanin su

Jaridar Legit.ng ta ruwaito cewa, fitaccen attajirin da ya fi kowa dukumar dukiya a duniya, Jeff Bezos, ya saki Matar sa, MacKenzie bayan sun amince da sawwakewa junan su inda za ta samu N12.5trn a matsayin hasafi na rabuwa.

Bezos bayan ya auri Matarsa a shekarar 1993 sun samu tabarraki na 'ya'ya hudu. A halin yanzu sun amince da sawwakewa junan su inda hasafin rabuwa da Mackenzie za ta samu zai sanya ta a mataki na uku cikin jerin Matan da suka fi kowa kudi a duniya.

Babban Hasafi: Mai kudin Duniya, Jeff Bezos, ya saki Matarsa
Babban Hasafi: Mai kudin Duniya, Jeff Bezos, ya saki Matarsa
Source: Getty Images

Kididdigar mujallar Forbes ta bayyana cewa, Bezos ya na ci gaba da samun dukiya a Amazon, kamfanin sa na gudanar da hada-hadar kasuwancin duniya ta hanyar fasahar zamani mai tushe a kasar Amurka.

Bezos da Mackenzie sun amince da rabuwa a tsakanin su yayin da suka bayar da sanarwar ci gaba da goyon bayan junan su da sabunta kyakkyawar alaka ta zumunta duk da rashin aure a tsakanin su.

KARANTA KUMA: Buhari tubalin karamci ne a duniya - Onochie

Yayin rabuwar su duba da irin gudunmuwar da ta bayar wajen fadi tashi a kamfanin Amazon, Mackenzie ta cancani samun kaso 4 cikin 100 na dukkanin kadarorin da ya kunsa da ya kai na kimanin Naira Tiriliyan 12.5.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na dandalan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit.ng News

Online view pixel