Kwankwaso, Tinubu, Saraki, da tsofaffin Gwamnoni 5 da su ke tashe yau duk da ba su kan mulki

Kwankwaso, Tinubu, Saraki, da tsofaffin Gwamnoni 5 da su ke tashe yau duk da ba su kan mulki

Duk da sun rabu da kujerar gwamnati, akwai wasu manyan ‘yan siyasa a Najeriya da ko a yau aka nemi gayya, za su fito da dinbin mabiya, ‘yan a-mutunsu.

Wasu daga cikin wadannan ‘yan siyasa da sun rike kujerar gwamnoni a jihohinsu, su na neman su fi gwamnonin da su ke kan mulki farin jini da mabiya a yau.

Legit.ng ta tattaro maku jerin irin wadannan zakakuran ‘yan siyasa da tauraruwarsu ba ta dushe ba:

1. Asiwaju Bola Ahmed Tinubu

Kusan babu wanda ya kafa yaransa a siyasa a wurare da-dama irin Bola Ahmed Tinubu. Tun daga saukarsa gwamnan Legas a 2007 zuwa yau, sai dai ma a ce mutanensa kara yawa su ke yi.

A jihar Legas ya yi sanadiyyar fito da magadansa uku, sannan yayi ruwa da tsaki wajen tsaida gwamnonin APC a wasu jihohi. Akwai manyan gwamnatin tarayya da ke rawa da bazarsa.

Kara karanta wannan

Dalilin Na Yasa Muka Nemi Afuwar Yan Najeriya Kan Yadda Muka Gudanar Da Mulki, Aisha Buhari

KU KARANTA: Tsohuwar minista Ezekwesili, ta soki DSS, mulkin Buhari

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

2. James Onanefe Ibori

Wani gawutaccen ‘dan siyasa a yankin Kudu maso kudu shi ne James Ibori. Tsohon gwamnan na Delta ya yi mulki tsakanin 1999 da 2007, amma har gobe sai yadda ya ce ake yi a yankinsa.

Duk da ya na gidan yarin kasar waje a shekarun baya, sai yadda James Ibori ya ce ake yi a Delta. Kusan duk kowane ‘dan siyasa da yake jin shi ya-isa, sai da ya je ya nemi mubaya’ar Ibori.

3. Bukola Saraki

Abubakar Bukola Saraki ya rike daular mahaifinsa a jihar Kwara. Rashin mulki bai sa an manta da tsohon gwamnan ba. Har yanzu Saraki ya na da mabiya da su ka shirya mutuwa domin shi.

Likitan ya rabu da harkar kiwon lafiya, ya shiga siyasa. Tun bayan nan ya zama hadimin shugaban kasa, gwamna, sanata, har ya rike matsayin shugaban majalisar dattawa.

Kara karanta wannan

Kwankwaso @66: Wasu abubuwa 10 da ba ka sani ba a game da ‘Dan Takaran NNPP

Kwankwaso, Tinubu, Saraki, da tsofaffin Gwamnoni 5 da su ke tashe yau duk da ba su kan mulki
Babban jigon APC, Bola Tinubu Hoto: Twitter
Asali: Facebook

KU KARANTA: Gwamnatin Tarayya ta ribanya adadin matasan da za a ba aikin N-Power

4. Sule Lamido

Alhaji Sule Lamido ya na cikin gawurtattun ‘yan PDP kuma ‘yan adawar gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari. Ko da ya bar gwamnati, mutanen Jigawa ba su manta da Sule ba.

Sule Lamido ya yi mulki ne tsakanin 2007 da 2015, lokacin da APC ta karbi gwamnati. Wannan ya sa tsohon Ministan bai yi nasarar ganin ‘dan takararsa na jam’iyyar PDP ya gaje sa ba.

5. Rabiu Kwankwaso

Idan ana maganar ‘dan siyasa da yake da tarin mabiya a Najeriya, za a kawo Madugun darikar Kwankwasiya, Sanata Rabiu Kwankwaso, wanda ya gaji tambarin jar hular Aminu Kano.

Rabiu Kwankwaso ya yi mulki a Kano sau biyu, tun wannan lokaci ya jawo wa kansa farin jini a jiharsa da kewayen Arewacin Najeriya. Mabiyansa na Kwankwasiyya sun shiga ko ina.

Kara karanta wannan

Ambaliya: Peter Obi Ya Gana da Wani Gwamnan Arewa, Ya Aike da Muhimmin Sako Ga Tinubu, Atiku da Kwankwaso

Asali: Legit.ng

Online view pixel