Da dumi: Wasu Malaman addini da tsaffin yan siyasa na son yiwa Buhari juyin mulki, Fadar shugaban kasa

Da dumi: Wasu Malaman addini da tsaffin yan siyasa na son yiwa Buhari juyin mulki, Fadar shugaban kasa

- Fadar shugaban kasa ta yi martani kan jawabin da hukumar DSS tayi

- DSS ta gargadi Malaman addini da sauran jama'a kan kira ga tsige shugaba Buhari

- Wannan ya biyo bayan kiraye-kirayen da ake yi ga shugaba Buhari ya sauka ko a tsigeshi

Fadar shugaban kasa ta bayyana cewa wasu Malaman addini da tsaffin yan siyasa na kokarin hada baki da wasu yan bakin haure wajen yiwa gwamnatin Buhari juyin mulki.

Fadar shugaban kasan ta ce an samu hujjoji kan shirin da ake yi na hada baki da wasu shugabannin kabilu da yan siyasa wajen alanta rashin imaninsu da shugaba Buhari.

Mai magana da yawun shugaban kasa, Femi Adesina, ya bayyana hakan a jawabin da ya saki ranar Talata.

"Wani shiri da wasu Malaman addini da tsaffin shugabanni ke yi, ana niyyar jefa kasar cikin rudani da rikici, wanda hakan zai tilasta yin juyin mulki," jawabin yace.

"Wasu karin hujjoji sun bayyana cewa wadannan mutanen yanzu haka na kokarin shawo kan shugabannin wasu kabilu da yan siyasa a kafin tarayya, da niyyar shirya wani taro inda za'a nuna rashin amincewa da shugaban kasa, wanda hakan zai jefa kasar cikin rikici."

DUBA NAN: An Kama Soja da Harsashi Sama da 2000 a Tashar Mota a Maiduguri

Da dumi: Wasu Malaman addini da tsaffin yan siyasa na son yiwa Buhari juyi mulki, Fadar shugaban kasa
Da dumi: Wasu Malaman addini da tsaffin yan siyasa na son yiwa Buhari juyi mulki, Fadar shugaban kasa Hoto: Femi Adesina
Asali: Facebook

DUBA NAN: An bankado badakalar kimanin N40bn a kasafin kudin 2021 da gwamnatin Buhari tayi

A bangare guda, Hedkwatar tsaro (DHQ) ta gargadi Sojoji da yan siyasa kan suyi hattara da kowani irin shirin yiwa gwamnatin shugaba Buhari juyin mulki.

Kakakin hedkwatar, Birgediya Janar Onyema Nwachukwu, ya yi wannan gargadi ne a jawabin da ya saki a Abuja ranar Lahadi, 3 ga Mayu, PRNigeria ta ruwaito.

Nwachukwu ya ce hukumar Soji ta samu labarin cewa wani ya bada shawaran mika mulki ga Sojoji domin yiwa kasa garambawul.

Asali: Legit.ng

Online view pixel