Ramadan: Babban Malami, Kabiru Gombe ya yi kira ga Buhari, Gwamnoni da babbar murya
- Sheikh Muhammad Kabiru Haruna Gombe ya yi kira ga shugaban kasa da Gwamnoni
- Malamin ya ba masu mulki shawara su fito da kudi, su taimaka wa al'ummarsu da binci
- Shehin ya ce hakan ne hanya mai sauki da za a bi, a kawo karshen masu satar mutane
Fitaccen malamin addinin nan, Muhammad Kabiru Haruna Gombe, ya yi kira ga shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya duba halin da al’umma su ke ciki.
A wajen darashin tafsirin da yake gabatar wa, Sheikh Muhammad Kabiru Haruna Gombe, ya yi kira ga shugaban Najeriya ya buda baitul-malin gwamnati.
Kabiru Haruna Gombe ya bukaci shugaban kasa da kuma gwamnonin jihohi su fito da kudi da nufin ba talakawa kayan abincin da za su ci a watan azumu.
KU KARANTA: Mahaifiyar Sheikh Kabiru Gombe, rasuwa ta rasu
“A bude baitul-mali, a saya wa talakawa tireloli na kayan abinci; shinkafa ta rika yawo, ana ba talakawa.”
“Ya ku gwamnonin jihohi, ku bude baitul-mali, a saya wa talakawa abinci a lokacin Ramadan. A fitar da dukiyar talakawa, a saya masu abinci saboda Allah.”
Shararren malamin kungiyar Jama’atul Izalatul Bidi’at wa Iqamatus Sunnah ya ba gwamnatin kasar shawarar yadda za a magance matsalar satar mutane.
Sheikh Gombe ya ce: “Masu garkuwa da mutane sun addabe ku, su na ta kashe miliyoyi a kan tsaro domin ku tsare al’umma, amma har yau babu nasara.”
KU KARANTA: Mun jawo hankalin ‘Yan Majalisan APC zuwa PDP – Hon. Elumelu
“Ga hanya mai sauki da za ku yi nasara, ku ji tausayin na-kasa, idan ku ka yi haka, Allah zai ji tausayinku.”
Sakataren na Jama’atul Izalatul Bidi’at wa Iqamatus Sunnah wanda aka fi sani da Izala, ya ce idan shugabanni su ka tausaya wa talakawansu, to Allah zai jikansu.
Malamin ya yi wannan bayani ne a tafsirin da yake gudanar wa na a bana tare da Alaranma Ahmad Sulaiman a masallacin ‘Yan lilo a Tudun Wada, Kaduna.
A shekarun baya kun ji cewa wani babban malami, Muhammad Garba Binkola ya nemi kungiyar Izala ta kwabi Shaikh Kabiru Gombe a kan irin kalaman da ya ke yi.
Sakataren Kungiyar ‘Tijjaniyya International Islamic Brotherhood’ ta duniya, Garba Binkola ya ce bai kamata Kabir Gombe ya rika bata ‘yan Darikarsu ta Tijjaniyar ba.
Asali: Legit.ng