An bankado badakalar kimanin N40bn a kasafin kudin 2021 da gwamnatin Buhari tayi

An bankado badakalar kimanin N40bn a kasafin kudin 2021 da gwamnatin Buhari tayi

- An gano wasu badakala a kasafin kudin 2021 da shugaba Buhari ya rattafa hannu a watan Disamba

- A cewar BudgIT, an maimaita wasu ayyuka 316 na kudi N39.5bn da kuma wasu kura-kurai na rashawa

- Kungiyar ta yi kira ga gwamnatin tarayya ta yi gyara wajen shirya kasafin kudi

Wata kungiya mai zaman kanta, BudgIT, ta gudanar da bincike cikin kasafin kudin 2021 da shugaba Muhammadu Buhari ya rattafa hannu.

Bayan wannan bincike, BudgIT ta bankado an maimaita wasu manyan ayyuka 316 na kimanin kudi N39.5bn.

Legit.ng ta ruwaito cewa wannan na kunshe cikin jawabin da BudgIT da ta saki a shafinta na Tuwita ranar Talata, 4 ga Mayu.

Kungiyar ta kara da cewa 115 cikin wadannan ayyuka 316 da aka maimaita na cikin kasafin ma'aikatar lafiya.

Shugaban BudgIT, Gabriel Okeowo, ya bayyana cewa: "Binciken da muka gudanar a kasafin kudin 2021 ya nuna cewa an maimaita manyan ayyuka 316 na kimanin N39.15bn, kuma 115 na cikin wadannan ayyuka na faruwa ne a ma'aikatar lafiya."

"Wannan babban abin damuwa ne dubi ga irin matsalar da ke sashen kiwon lafiya da kuma annobar COVID-19 da ta addabi Najeriya."

A kasafin kudin 2021, kudi N1.97tn aka baiwa bangaren tsaro, Okeowo yace.

DUBA NAN: Isa Pantami Ya Tsawaita Wa’adin Hade NIN-SIM Har Zuwa 30 Ga Watan Yuni

An bankado badakalar kimanin N40bn a kasafin kudin 2021 da gwamnatin Buhari tayi
An bankado badakalar kimanin N40bn a kasafin kudin 2021 da gwamnatin Buhari tayi Hoto: @NGRPresident
Asali: Facebook

KU KARANTA: Muna tare da shugaba Buhari, Hedkwatar Soji ta yi watsi da shawaran juyin mulki

Kudin tsaro

BudgIT ta bankado cewa wasu ma'aikatu da basu da wata alaka da tsaro sun fara karban kudi don samar da tsaro.

Legit.ng ta tattaro cewa a kasafin kudin 2021, ma'aikatun gwamnatin tarayya 117 sun karbi kudin tsaro na kimanin N24.3 billion, duk da cewa an riga an basu wasu kudaden tsaro

BudgIT ta kara da cewa gaba daya kasafin kudi na cike da kura-kuran gayya don samun satan kudin al'umma.

A wani labarin kuwa, hedkwatar tsaro (DHQ) ta gargadi Sojoji da yan siyasa kan suyi hattara da kowani irin shirin yiwa gwamnatin shugaba Buhari juyin mulki.

Kakakin hedkwatar, Birgediya Janar Onyema Nwachukwu, ya yi wannan gargadi ne a jawabin da ya saki a Abuja ranar Lahadi, 3 ga Mayu, PRNigeria ta ruwaito.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng