DSS ta aike muhimmin sako ga masu hana zaman lafiya a Najeriya

DSS ta aike muhimmin sako ga masu hana zaman lafiya a Najeriya

- Hukumar DSS ta ce ba zata sake sassautawa masu kokarin tarwatsa Najeriya ba da hanata zaman lafiya

- Kakakin hukumar, Peter Afunanya, yace hukumar na goyon bayan cigaban hadin kan kasar nan tare da zamanta tsintsiya daya

- Hukumar tace tas take kallon wasu da ke amfani da banbancin addinai da siyasa wurin kokarin raba kasar nan

Hukumar jami'an tsaron farin kaya (DSS) ta ja kunnen miyagun jama'an da ke kokarin tarwatsa Najeriya da zaman lafiyanta da su gaggauta dena hakan.

Peter Afunanya, kakakin DSS, yace daga yanzu hukumar ba zata sake sassautawa duk wanda ta kama yana kokarin tarwatsa zaman lafiyan Najeriya ba.

A wata takarda da TheCable ta gani, yace: "Yayin da hukumar take cigaba da tabbatar da goyon bayanta ga Najeriya daya mai cike da zaman lafiya, ba za ta cigaba da lamuncewa duk wasu kungiyoyi ba masu fatan tarwatsa kasar da masu daukar nauyinta.

"Hakazalika, hukumar tana aiki tare da jami'an tsaro da sauran hukumomin tabbatar da doka wurin tabbatar da zaman lafiya da tsaron cikin gida Najeriya."

KU KARANTA: Mbaka ya bukaci kwangila bayan goyon bayan Buhari amma aka hana shi, Garba Shehu

DSS ta aike muhimmin sako ga masu hana zaman lafiya a Najeriya
DSS ta aike muhimmin sako ga masu hana zaman lafiya a Najeriya. Hoto daga @Thecableng
Asali: Twitter

KU KARANTA: Ndume: Najeriya bata mayar da hankali ba wurin shawo kan matsalar tsaro

Afunanya yace duk wasu masu barazana ga gwamnatin tarayya da hadin kan Najeriya sune wasu addinai da tsoffin shugabannin siyasa wadanda ke son ta karfin tsiya su sauya gwamnati.

"An gano cewa babban burninsu shine tarwatsa kasar nan," yace.

“Abun takaici ne yadda jama'a wadanda ake ganin mutuncinsu kuma ana zaton suna da kishi kasa ke kokarin ganin bayan Najeriya. Hukumar ta gano yadda suka kafu da ganin sun hada kai da wasu miyagu daga kasashen ketare domin tarwatsa kasar nan."

A wani labari na daban, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince da karin kudin 'yan fansho zuwa sabon karancin albashin kasar nan da aka duba a watan Afrilun 2019.

Ekpo Nta, mukaddashin shugaban hukumar albashi ta kasa (NSIWC) ya bayyana hakan yayin zantawa da manema labarai a garin Kalba, babban birnin jihar Cross Rivers a ranar Juma'a.

A watan Afirlun 2019, Buhari ya sa hannun kan sabuwar dokar karancin albashi. An kara daga N18,500 zuwa N30,000 a matsayin mafi karancin albashi a kasar nan.

Asali: Legit.ng

Online view pixel