Najeriya ta yi rashin babban Soja, wasu mutane da kayan yaki a hare-haren ‘Yan Boko Haram
- An hallaka wani babban Soja a harin da Boko Haram su ka kai a garin Ajiri
- A ‘yan makonnin nan da su ka wuce, ‘yan ta’adda sun addabi yankin Borno
- Bayan nan, Mayakan Boko Haram sun yi gigin kai wani harin a garin Rann
Wani shugaban dakarun sojojin kasa da wasu manyan jami’ai bakwai sun mutu a lokacin da ‘yan ta’addan Boko Haram su ka kai hari a jihar Borno.
Jaridar Daily Trust ta fitar da rahoto a ranar Lahadi cewa ‘yan ta’addan sun sake kai hari kamar yadda su ka matsa wa jama’an Arewa maso gabas.
A safiyar Lahadi, 2 ga watan Mayu, 2021, ‘yan ta’addan Boko Haram su ka kai hari a sansanin sojoji da ke garin Ajiri da ke kilomita 20 da Maiduguri.
KU KARANTA: ISWAP sun kai mumunan hari a barikin Sojoji a Yobe
Dakarun Islamic State West Africa Province na kungiyar Boko Haram ne ake zargi da wannan aiki.
‘Yan ta’addan sun dura garin Ajiri ne a kan babura da motocin yaki, su ka kai wa sojoji hari, har su ka tsere. An dauki sa’o’i akalla biyu ana fafata wa a garin.
Wani jami’in soja ya fada wa ‘yan jarida: “Shugaban dakarun sojojin ya kwanta dama, yayin da masu fararen kaya shida da ta rutsa da su, su ka mutu.”
A wata majiyar, an tabbatar da cewa mayakan Boko Haram sun dauke makaman sojojin Najeriya.
KU KARANTA: Gwamnonin Arewa sun yi wa Rundunar Sojoji ta'aziyya
Kafin nan an kai wani hari a ranar Asabar, inda ‘yan ta’addan su ka yi nasarar auka wa garin Rann. Jami’an sojoji sun tabbatar da wannan harin a jiya.
“Sun zo da motocin yaki shida, sai su ka gamu da rundunar sojoji. Sojojin kasa sun yi wa wasu biyu daga cikin motocin yakin da su ka zo luguden wuta.”
Sauran mayakan ‘yan ta’addan sun tsere daga Rann ganin dakarun Najeriya sun fi karfinsu. Daga baya wani mutum da aka yi wa rauni, ya mutu a gadon asibiti.
Dazu nan ku ka samu rahoto cewa a lokacin da ake fama da kashe-kashe, rundunar 'yan sandan jihar Ebonyi ta kama wasu miyagun makamai masu hatsari.
Kamar yadda mu ka ji, ‘yan sanda sun kama harsasan GPMG 753 a wata motar haya da ta tashi daga garin Abakaliki za ta isa babban birni Umuahia na jihar Abia
Asali: Legit.ng