Buhari ya bada sanarwar fadada shirin N-Power domin ‘Ya ‘yan Talakawa su amfana
- Gwamnatin Tarayya ta bayyana yadda ta taimakawa matasa da marasa galihu
- Shugaba Muhammadu Buhari ya ce an ribanya adadin masu yin aikin N-Power
- Yanzu matasa miliyan daya za su ci moriyar shirin N-Power da aka fito da shi
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ce gwamnatinsa za ta fadada wadanda za su mori tsarin N-Power da aka shigo da shi, domin matasa su amfana.
Jaridar PM News ta ce Muhammadu Buhari ya bayyana cewa yanzu za a kara adadin matasan da su ke cikin wannan tsari daga mutum 500, 000 zuwa 1, 000, 000.
Shugaban kasar ya yi wannan bayani ne a jawabinsa da ya fitar domin taya al’umma murnar ranar ma’aikata ta kasa a ranar Asabar, 1 ga watan Mayu, 2021.
KU KARANTA: Gwamnati Tarayya ta fitar da sanarwar wasu nade-naden mukamai
Mai girma Muhammadu Buhari ya yi wa bikin shekarar nan da taken: “Annobar COVID-19: Kalubale wajen samun walwala da jin dadin ma’aikata.”
Muhammadu Buhari ya ce fadada tsarin N-Power zai taimaka sosai wajen samar da aikin yi da yaki da talauci a lokacin da ake fama da annobar COVID-19.
Gwamnatin tarayya ta kawo wannan shiri na N-Power ne a 2016 domin inganta rayuwar matasa.
Shugaban kasar ya ce an fadada tsarin tattalin arziki da zamantake wa na bada kudi a gidaje miliyan 7.6 daga gidaje miliyan 2.6 na marasa galihu da aka yi a da.
KU KARANTA: Ganduje ya kara shekarun ritayar Malaman Makaranta a Kano
Da wannan shiri, mutane miliyan 32 za su amfana da gwamnati, akasin miliyan 13 da su ka mora a baya.
Bayan haka gwamnati ta shigo da tsarin bada tallafin COVID-19 RRR wanda zai tallafa wa talakawa da masu karamin karfi akalla miliyan 20 da ke birane.
Sannan kuma ma’aikatar masana’antu da zuba jari da kasuwancin tarayya ta shigo da tsare-tsaren bada jari da zai taimaka wa kananan ‘yan kasuwa a kasar.
A wajen karatunsa na tafsiri a Kaduna, Sheikh Kabir Gombe ya fadi hanyar da za a bi domin ayi maganin masu garkuwa da mutane da talaucin da ake fama da shi.
Kabir Gombe ya ce hanya mafi sauki da shugabanni za su bi, su kawo karshen satar mutanen da ake yi shi ne a tausaya wa talakawan da su ke jagoranta a Najeriya.
Asali: Legit.ng