Nasihohi guda 50, Daga Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa Kano

Nasihohi guda 50, Daga Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa Kano

Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa babban Malamin addinin Musulunci ne mazaunin jihar Kano wanda ya fi shahara wajen bayani kan mas'alolin rayuwa da zamantakewa.

A wannan karo, Malamin ya lissafo abubuwa 50 a saukake yda ya kamata Musulmi yayi don tsira a duniya da lahira

Ga jerinsu:

1. Ka kula da kanka

2. Ya zamana kana jin tsoron Allah

3 Ka san cewa duk abinda ya sameka daga Allah ne

4 Ka zamu mai cika alkawari

5 Ka zauna da kowa lafiya

6 Ka dinga tunawa da mutuwa

7 Ka rage buri

8 Ka cire kwadayi

9 Banda yin hassada don kaga Allah ya daukaka wani

10 Kasan cewa ita fa duniya ba matabbaciya bace

11 Ka yawaita istigifari

12 Ka yawaita salati ga manzon Rahama

13 Banda yin gulma ko munafurci

14 Banda cin amana

15 Ka zauna da kowa lafiya

16 Ka tsarkaka zuciyarka

17 Banda nufar mutum da sharri

18 Karkayi zalunci

19 Karkayi girman kai

20 Karkayi wulakanci

21 Ka zama mai taimako

22 Ka kula da addininka

23 Ka zamu mutum mai Alkunya

24 Ka zama mutum nagari mai kirki

25 Kasan cewa komai mai wucewa ne

Nasihohi guda 50, Daga Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa Kano
Nasihohi guda 50, Daga Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa Kano Credit: Mal.Aminu Ibrahim Daurawa
Asali: Facebook

26 Ka dinga hakuri kar ama shaidar cewa baka da hakuri

27 Ka kuma yawaita addu'a

28 Kayi biyayyah ga iyayenka

29 Ka zama mai tausayi

30 Ka zama mai imani

31 Kana aiki da hankalinka

32 Ka guje wa sabon Allah

33 Karka ci haram

34 Karkayi shaye-shaye

35 Ka nisanci zina

36 Ka mai da hankalinka guri daya

37 Ka ciyar da kanka halal

38 Karka zama mutum mai yaudara

39 Duk abinda zakayi kayi saboda Allah

40 Banda aibatan mutum don kaga yana wani yanayi,yi mishi addu'a

41 Ka zama mai taimako da tausayin iyayenka

42 Ka yawaita yiwa wadanda suka rasu addu'a

43 Kazama mutumin da kowa zai dinga maka kyakkyawar shaida

44 Kabi duniya a hankali

45 Karka dinga yin gaggawa

46 Sannan ka rike gaskiya duk maganar dazaka fada kake yin gaskiya.

47 Ka zama mai adalci a duk inda kake

48 Kar abin duniya ya rudeka har kaje kana aikata sabo

49 Ka kula da hakkin makwaftanka

50 Kayi fatan gamawa da duniya lafiya...

Allah Yasa mudace

Asali: Legit.ng

Online view pixel