Labari da dumi-dumi: Shugaba Buhari ya fitar da sababbin nadin mukamai a Gwamnati
- Fadar Shugaban kasa ta fitar da jerin sababbin nade-naden mukamai a dazu
- An nada darektocin da za su kula da hukumomin ma’aikatar labarai da al’adu
A yau Juma’a, 30 ga watan Afrilu, 2021, fadar shugaban kasa ta bada sanarwar wasu nade-naden mukamai da aka yi a ma’aikatar yada labarai da al’adu.
Kamar yadda mu ka fahimta, mutane hudu ne aka ba mukamai da yamman yau. Uku daga cikinsu za su zarce ne a kujerunsu, daya sabon shiga ne.
Wadanda aka ba wadannan kujeru za su yi shekaru hudu a ofis, za su sauka a shekarar 2025.
Ga wadanda aka ba mukaman nan kamar haka:
KU KARANTA: Gwamnonin APC sun ziyarci ofishin IGP a kan batun tsaro
1. Otunba Segun Runsewe (NCAC)
Otunba Segun Runsewe ya zarce a kan kujerar babban darektan hukumar al’adu da fasaha watau NCAC.
2. Folorunso Coker (NTDC)
Folorunso Coker zai cigaba da rike kujerarsa ta babban darektan hukumar bunkasa sha’anin buda ido na kasa.
3. Alhaji Adedayo Thomas (NFVCB).
Haka zalika Alhaji Adedayo Thomas ya koma kan mukaminsa na shugaban hukumar tace fim da bidiyo na kasa
KU KARANTA: Majalisa za ta kebe kujeru 111 na musamman domin mata
4. Ahmed Mohammed Ahmed
Shugaban Najeriya ya kuma amince da nadin Alhaji Ahmed Mohammed Ahmed a matsayin darektan yada al’adu.
Kafin samun wannan matsayi, Ahmed Mohammed Ahmed darekta ne a ma’aikatar yada labarai da shakatawa na jihar Bauchi.
A yau ne Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya jagoranci wani taron majalisar tsaro na kasa a fadar Aso Rock da ke Abuja.
Wadanda suka halarci su ne; mataimakin shugaban kasa, sakataren Gwamnatin Tarayya, hafsoshin tsaro da wasu Ministoci.
Asali: Legit.ng