Allah ya yiwa mahaifiyar babban malamin addini, Sheikh Kabiru Gombe, rasuwa

Allah ya yiwa mahaifiyar babban malamin addini, Sheikh Kabiru Gombe, rasuwa

- Inna lillahi wa inna ilaihi raji'un

- Za'ayi Sallar Jana'izarta misalin karfe 1:30 na rana bayan Sallar Juma'a a a Bolari

Shahrarren Malamin addini kuma sakataren kungiyar Jama’atul Izalatul Bid’a WaIqamatus Sunnah, JIBWIS, Sheikh Kabir Haruna Gombe, ya yi rashin mahaifiyarsa, Fatima Abdullahi-Haruna.

Hajiya Fatima ta rasu ne bayan shekaru 75 a duniya.

Diraktan dandalin sada zumuntan JIbwis, Ibrahim Baba-Suleiman, ya sanar da hakan a shafin Facebook da yammacin Alhamis, Daily Nigerian ta gano.

A cewarsa, Hajiya ta rasu ne da yammacin Alhamis a wani asibiti dake jihar Gombe bayan dogon rashin lafiya.

Ya kara da cewa za'ayi jana'izarta bayan Sallar Juma'a ranar 30 ga wata a Masallacin JIBWIS dake Bolari, jihar Gombe.

DUBA NAN: Hanan Buhari da Mijinta Muhammad Turad sun saki hotunansu na farko bayan aure

Allah ya yiwa mahaifiyar babban malamin addini, Sheikh Kabiru Gombe, rasuwa
Allah ya yiwa mahaifiyar babban malamin addini, Sheikh Kabiru Gombe, rasuwa Hoto: @dailynigerian
Asali: Twitter

KU KARANTA: Ba yunwa ta sa ake satan kayan tallafin Korona ba, kwadayi ne kawai - Fadar shugaban kasa

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel