"An samu ‘Yan APC da su ka kammala shirin yadda za su fice zuwa PDP kafin zaben 2023"

"An samu ‘Yan APC da su ka kammala shirin yadda za su fice zuwa PDP kafin zaben 2023"

- Hon. Ndudi Elumelu ya shaidawa PDP wasu ‘Yan Majalisar APC za su sauya-sheka

- Ndudi Elumelu ya yi wannan bayanin ne a wajen taron NEC da PDP ta shirya a jiya

- ‘Dan Majalisar ya ce wasu abokan aikinsu sun gamsu su dawo tafiyar jam’iyyar PDP

Shugaban marasa rinjaye a majalisar wakilan tarayya, Hon. Ndudi Elumelu, ya bayyana cewa akwai wasu masu zawarcin jam’iyyarsu ta PDP.

A cewar Honarabul Ndudi Elumelu, wasu ‘yan majalisa na jam’iyyar APC sun kammala shirye-shiryen yadda za su koma PDP kafin zaben 2023.

Vanguard ta rahoto Ndudi Elumelu ya na cewa ‘yan majalisar sun dauki matakin ne domin ceto al’ummar kasar nan daga damkar da APC ta ke yi.

KU KARANTA: Za a dakatar da Shugaban APC saboda hada-kai da Tinubu

Bayanin Elumelu ya shiga hannun ‘yan jaridar da ke aiki a fadar majalisar tarayya ne bayan ya yi wannan jawabi a wajen taron NEC na jam’iyyar PDP.

Elumelu ya ce gwamnatin APC ta ruguza duk nasarorin da jam’iyyar PDP ta samu a kan mulki.

“An kafa jam’iyyarmu ne a kan turaku masu karfi na hadin-kai da tafiya da kowa, tare da bin doka da tsarin mulki, adalci, da yin gaskiya, girmama wa, cigaban tattalin arziki, walwala, tsaro da jin dadin kowa.” Inji Elumelu.

Hon. Elumelu yake cewa PDP ta kokarta wajen bunkasa tattalin arzikin Najeriya da gina abubuwan more rayuwa da hada-kan jama’a a shekaru 16.

KU KARANTA: Ana shirin warewa Mata kujeru fiye da 100 a Majalisa

"An samu ‘Yan APC da su ka kammala shirin yadda za su fice zuwa PDP kafin zaben 2023"
Hon. Ndudi Elumelu @RepsNgr
Asali: Twitter

"Abin bakin ciki, a cikin shekaru shida, gwamnatin APC maras gaskiya, maras tausayi da imani, da rashin sanin kan aiki ta ruguza duk wadannan nasarorin."

Mafitar magance wadannan matsaloli na rashin gaskiya shi ne a dawo da PDP mulki a 2023, a cewar sa.

A dalilin kokarinsu, Elumelu ya ce wasu daga cikin abokan aikinsu da ke jam’iyyar APC sun ga dalilin sauya-sheka zuwa PDP domin a ceci kasa a zaben 2023.

Tsohon Sanatan APC, Godswill Akpabio ya ce matsalar siyasa ta shiga cikin lamarin rashin tsaron da ya ki ci, ya ki cinyewa har gobe a wasu jihohin Najeriya.

Tsohon Gwamnan na jihar Akwa Ibom ya ce dole a binciko masu tada kafar baya. Sanata Godswill Akpabio ya bayyana wannan ne yayin da ya ziyarci ofishin APC.

Asali: Legit.ng

Online view pixel