Siyasa-da-malanta: Wani malami ya bukaci a ja kunnen Sheikh Kabiru Gombe
Wani babban malami da kuma ke zaman Sakataren Kungiyar ‘Tijjaniyya International Islamic Brotherhood’ ta duniya, Malam Muhammad Garba Binkola ya nemi kungiyar Izala ta kwabi Shaikh Kabiru Gombe akan irin kalamansa akan batun zabar Buhari.
Malam Muhammad Garba wanda ke zama a garin Kaduna ya yi wannan Kira ne a cikin wata sanarwa da ya raba wa manema labarai a Kaduna cikin makon nan. Inda ya bayyana cewa bai kamata Kabir Gombe, wanda shi ne Sakataren Izala ta kasa ya rika furta kalamai da nufin ba ta ‘yan Darikar Tijjaniyar ba.
KU KARANTA: Wanda musulmi ya kamata su zaba - Wani malamin adddini
Legit.ng Hausa Shaihin Malamin ya ce su ‘yan Tijjaniya ba a sansu da neman tashin hankali ba, don haka ne ma ya sa ya bukaci shugabannin Izalar da su dauki mataki.
Ya ce, “Mu masu dogaro ne da kanmu ba dan wani ya sammans ba. Muna kuma yin ikilasi domin Allah da kuma ma’aiki Manzon Allah.
Wannan furuci na Kabiru Gombe bai dace ba domin yanzu akwai Muruden mu dake sama da ni su suka aikomin da wannan labari domin in gani in kuma ji abin da shi Kabiru Gomben ya ce.
A 'yan kwanakin nan dai shigar malamai harkokin siyasa a kasar nan tsamo-tsamo ya hairfar da rarrabuwar kawunan al'umma musamman ma mabiyan su yayin da kuma ake ta bayyana ra'ayoyi mabanbanta game da dacewar hakan.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com
Asali: Legit.ng