Karancin mata: Ana shirin warewa Mata kujeru fiye da 100 a Majalisar Tarayya da Jihohi

Karancin mata: Ana shirin warewa Mata kujeru fiye da 100 a Majalisar Tarayya da Jihohi

- Hon. Nkeiruka Onyejeocha ta na so a ware wasu kujeru saboda mata a Majalisa

- Kudirin da aka gabatar domin kara kujeru ya tsallake mataki na biyu a Majalisa

- Idan an yi nasara, adadin kujerun majalisar tarayya zai karu daga 369 zuwa 480

Majalisar wakilan tarayya ta fara shirin samar da kujeru na musamman ga mata a majalisar dattawa da ta wakilai da na dokoki da ke jihohin fadin kasar nan.

Jaridar Daily Trust ta fitar da rahoto cewa Hon. Nkeiruka Onyejeocha ta gabatar da wani kudiri da zai ba mata samun damar wakiltar al’umma a majalisun Najeriya.

Wannan kudiri ya na neman ya yi garambawul ga wasu sassan kundin tsarin mulkin kasa na 1999.

KU KARANTA: Jami’an DSS sun kama tsohon 'Dan Majalisa a kan sukar Gwamnati

‘Yar majalisar ta APC ta na neman canza sassa na 48; 49; 71; 77; 91; da 117 na kundin tsarin mulki domin ayi maganin karancin mata da ake da su yanzu a majalisa.

Mataimakiyar shugabar mai tsawatarwa a majalisar wakilan, Nkeiruka Onyejeocha, ta bijiro da wannan kudiri domin 'yanuwanta mata su rika wakiltar al'umma.

Hon. Onyejeocha ta ce idan kudirin da ta kawo ya samu karbuwa, za a rika ware wasu kujeru na musamman a gefe wanda mata ne kurum za su shiga takarar cinsu.

A cewar ‘yar majalisar ta Abia, za a dauki irin wannan salo na wucin-gadi a majalisar tarayya da na dokoki a matsayin dabarar da za ta sa a rika yi da mata a siyasa.

KU KARANTA: Jajirtattun 'yan siyasa mata 5 da su ke tashe a Najeriya

Jamilu Muhammad, wanda ya taba neman takarar majalisa a jihar Neja ya ce ganin mata a majalisu ya na da kyau, amma a kirkiro masu kujeru ba daidai ba ne.

A cewar Jamilu Muhammad, shiga majalisa wakilci ne na jami’a, ya ce wannan ita ce sunnar tsarin farar hula, akasin haka zai sa mata su rika samun kujeru a bagas.

A hirar da ya yi da Legit.ng, ya ce idan aka ware kujeru, aka ba mata kyauta, an saba wa tsarin damukaradiyya, domin kamata kowa ya shiga zabe, ya tallata kansa.

Karancin mata: Ana shirin warewa Mata wasu kujeru fiye da 100 a Majalisar Tarayya da Jihohi
Hon. Nkeiruka Onyejeocha mai wakiltar Isuikwuato da Umunneochi
Asali: Twitter

Wannan kudiri na Nkeiruka Onyejeocha ya tsallake matakin sauraro na biyu a zaman da aka yi jiya. Idan kudirin ya karbu, kujerun majalisa za su tashi zuwa 480.

Onyejeocha ta na so a ware wa mata karin kujerar majalisar dattawa a jihohi 36 da birnin tarayya, sannan za a ba mata kujeru biyu a majalisar wakilai a kowace jiha.

A yau matan da ke majalisar wakilan tarayya da dattawa ba su kai 5%, kusan mafi karanci a Duniya.

Kwanakin baya mun kawo maku jerin wasu fitattun 'yan siyasa mata da ake sa ran tauraruwarsu za ta haska a zaben 2023. Daga cikinsu akwai Sanata Abidoun Olujimi.

Ragowar su ne 'yar siyasar Kogi, Natasha Akpoti, Sanata Uche Ekwunife, karamar Ministar sufuri, Gbemisola Saraki, da kuma shugabar NPA ta kasa, Hadiza Bala Usman.

Asali: Legit.ng

Online view pixel