Ministan Buhari ya fallasa masu hannu a tabarbarewar matsalar tsaro da aka samu

Ministan Buhari ya fallasa masu hannu a tabarbarewar matsalar tsaro da aka samu

- Sanata Godswill Akpabio ya na ganin akwai siyasa a sha’anin rashin tsaro

- Ministan ya bayyana wannan ne a lokacin da ziyarci Hedikwatar APC jiya

- Tsohon Gwamnan Akwa Ibom ya bukaci a binciki masu tada zaune-tsaye

Mai girma Ministan harkokin Neja-Delta, Godswill Akpabio, ya furta albarkacin bakinsa a game da matsalar rashin tsaro da ake fama da ita.

Da yake magana, Godswill Akpabio ya bayyana cewa akwai burbushin siyasa a game da aika-aikan da ‘yan bindiga su ke yi a fadin kasar nan.

Daily Trust ta ce Sanata Godswill Akpabio ya yi wannan bayani a ranar Alhamis lokacin da ya zanta da ‘yan jarida da ya ziyarci hedikwatar APC.

KU KARANTA: A kira taron gaggawa a kan batun tsaro - PDP

“Ina ganin duk abubuwan da su ke faruwa su na da alaka da siyasa.” Inji Ministan na Neja-Delta.

“Saboda haka dole mu yi amfani da madubin duba-rudunmu, mu gano matsalar, mu bankado wadanda su ka jefa mu cikin halin da mu ke ciki.”

Godswill Akpabio ya kara da cewa: “Abin da ya kare faruwa yanzu ba a jinin Najeriya ba ne.”

Yace yanzu ba lokaci ne na jifan juna da zargi ba. “Dole mu yi duk abin da za mu iya, ko da ta shawarwari ne, mu tabbatar Najeriya ta zauna a dunkule.”

KU KARANTA: Zargin Shugaban PDP da cin kudi ya jawo ana barazanar shiga kotu

Akpabio bayyana makusudin zuwansa babban ofishin jam’iyyar APC, ya ce ya zo ne domin ya jaddada mubaya’arsa ga shugabancin Mai Mala Buni.

Tsohon gwamnan Akwa Ibom yake cewa ya ziyarci hedikwatar ne domin ya ba shugabannin rikon kwarya shawarar yadda za su tafiyar da jam’iyya.

Kafin yanzu kun samu labari cewa Gwamnonin Kebbi da Ekiti, Atiku Bagudu da Kayode Fayemi sun ziyarci ofishin IGP bayan an hallaka wasu ‘Yan Sanda.

Wadannan gwamnoni na APC sun yi zama na musamman da sabon Sufetan ‘Yan Sandan a kan matsalar kashe-kashen da ake fama da su a jihohi da-dama.

Asali: Legit.ng

Online view pixel