Rashin tsaro: PDP ta kira taron gaggawa, ta fadawa Buhari abin da ya kamata ya yi

Rashin tsaro: PDP ta kira taron gaggawa, ta fadawa Buhari abin da ya kamata ya yi

- Jam’iyyar PDP ta ce sha’anin rashin tsaro ya addabi al’umma yanzu a Najeriya

- Prince Uche Secondus ya ce idan babu zaman lafiya ba zai yiwu a shirya zabe ba

- PDP ta kira taron NEC na gaggawa, inda ta bada shawarar a kira taron masana

Shugaban jam’iyyar PDP na kasa, Prince Uche Secondus, ya yi gargadi cewa ba dole ba ne zaben 2023 saboda irin halin da ake ciki yanzu a Najeriya.

Prince Uche Secondus ya ce idan sha’anin tsaro ya tabarbare, zai yi wahala zabe ya yiwu. Jaridar Daily Trust ta fitar da wannan rahoto a ranar Alhamis.

Rahoton ya ce Prince Uche Secondus ya bayyana wannan ne a wani taron gaggawa da majalisar kolin jam’iyyar PDP ta kira a jiya a birnin tarayya Abuja.

KU KARANTA: Faston da ya yi wa Jonathan adawa, ya ce ‘Ubangiji ya yi fushi da Buhari’

Shugaban jam’iyyar adawar ya yi kira shugaba Muhammadu Buhari ya kira taron kasa na musamman kan sha’anin tsaro domin a samu zaman lafiya.

Wannan taro zai taimaka da shawari a kan yadda za a bijiro wa harkar tsaro a kasar inji Secondus.

Uche Secondus ya ce abin da ke faruwa yanzu ya na da ban-tsoro, ya ce akwai bukatar duk wasu masu ruwa da tsaki su zauna domin a samar wa kasa mafita.

“Duk surutun 2023 da ake yi zai kare a banza ne idan ba ayi hobbasa a kan sha’anin tsaro ba.”

KU KARANTA: ASUU ta ce karin 500% a kudin karatun KASU zai kora yara barkatai

Rashin tsaro: PDP ta kira taron gaggawa, ta fadawa Buhari abin da ya kamata ya yi
Shugaban PDP a taro

“Kasar mu a yau ta tsaya tsak saboda rashin tsaro, kuma babu martanin da gwamnati ta ke dauka duk da dokar kasa ta ce kare ran jama’a shi ne aikin hukuma.”

A cewar Secondus, ‘yan ta’addan da a baya su ka takaita a Arewa maso gabas sun bazu zuwa sauran sassan kasar, ya ce al’umma su na zaune cikin firgici a yau.

A baya kun ji cewa hamayyar Asiwaju Bola Tinubu da Kayode Fayemi a APC ta sa za a sallami wani shugaban SWAGA da ke rike da APC a mazabarsa daga Jam’iyya.

Kusancinsa da kungiyar da ke goyon bayan Bola Tinubu ya tsaya takara a 2023, ta sa manyan jam’iyyar APC na shirin dakatar da shugabanta a karamar hukumar Ado.

Asali: Legit.ng

Online view pixel