Faston da ya goyi bayan Buhari a zaben 2015 ya bukaci a tsige Shugaban kasa ko ya yi murabus
- Fr Ejike Mbaka ya ce ana fama da kashe-kashe, amma shugaban kasa ya yi tsit
- Limamin cocin na Adoration Ministry ya bukaci Shugaba Buhari ya yi murabus
- Ejike Mbaka ya yi kira ga Majalisa ta tsige Shugaban kasar idan ya yi taurin kai
Shugaban cocin Adoration Ministry da ke garin Enugu, Fr Ejike Mbaka, ya yi ikiarin Ubangiji ya na fushi da shugaban Najeriya Muhammadu Buhari.
Ejike Mbaka wanda ya na cikin wadanda su ka goyi bayan Muhammadu Buhari gabanin zaben 2015 ya nuna gwamnatin APC tayi sake da ran al'umma.
Daily Trust ta rahoto Ejike Mbaka ya na cewa ko dai shugaban kasar ya yi murabus, ko a tsige shi.
KU KARANTA: Mabiya cocin ECWA sun nemi Buhari ya ajiye mulki
Da yake magana a cocinsa a garin Enugu, Mbaka ya ce bai kamata shugaban kasa ‘ya yi gum’ a lokacin da ake ta kashe Bayin Allah a fadin kasar nan ba.
“Na san wasu za su ce, Mbaka ba ka yi wa Buhari addu’a ba. Me ku ke magana? Shin ni ne na hallacin Buhari? Ubangiji ne ya hallice sa.” inji limamin cocin.
Fasto Mbaka ya cigaba da cewa: “’Yan Najeriya su ka zabe shi saboda ya yi abin a-yaba a baya, amma a kan menene mutane za su cigaba da mutuwa haka nan.”
“Da a kasar da aka cigaba ne, da yanzu shugaban kasa ya ajiye aikinsa. Ka rubuta, ka ajiye, kowa ya ji. Shugaba Buhari ya yi murabus tun da girma, da arziki.”
KU KARANTA: Buhari bai damu da halin Najeriya ta ke ciki ba - PDP
Ya ce: “Idan ba za ka iya ba, sai ka yi murabus, ko a canza ka. Mai horaswa ba zai tsaya ya na kallo ana doke kungiyarsa ba, yayin da ‘yan wasa su ke wajen fili ba.”
“’Yan bindiga na ta kai wa kowa hari. Meyasa matasan Najeriya su ke kuka? Ana ta jibge matasan mu a kasar waje, Lauyoyi da Likitoci su na tsere wa can.” inji shi.
“Menene ke faruwa? Babu tsaro a ko ina. Idan ba zai sauka ba, ‘yan majalisar wakilai da sanatoci su tsige shi.” Ejike Mbaka ya ce Ubangiji ya yi fushi da shugaban.
A jiya ne shahararren malamin addinin musulunci, Sheikh Dahiru Usman Bauchi, ya fito, ya yi kira ga gwamnatin tarayya ta kawo karshen matsalar kashe-kashe.
Da yake magana a Kaduna, Dahiru Usman Bauchi ya bukaci gwamnati ta sauke nauyin da ke kanta na kare jama’a daga ‘yan bindigan da su ke bi, su na kashe al’umma.
Asali: Legit.ng