Bamu kara kudin makaranta ba, amma zamu kara: Jami'ar jihar Kaduna KASU

Bamu kara kudin makaranta ba, amma zamu kara: Jami'ar jihar Kaduna KASU

- Daliban jami'ar Kaduna sun lashi takobin zanga-zanga idan har aka kara kudin makaranta

- Shugabannin jami'ar sun ce zasu kara kudin makarantan amma basu sanar ba tukun

- A cewar wasu cikin daliban, kudin a yanzu ma da kyar wasu ke iya biya, ballanatan idan aka kara

Shugabannin jami'ar jihar Kaduna (KASU) sun yi watsi da rahotannin cewa an kara kudin makaranta kuma sun yi kira ga dalibai su kwantar da hankulansu.

A jawabin da mai magana da yawun makarantar, Adamu Bargo, ya saki ranar Alhamis, ya ce labaran karin da ake yadawa a kafafen ra'ayi da sada zumunta karya ne.

Wani sashen jawabinsa yace, "Shugabannin jami'ar jihar Kaduna na sanar da dalibai, iyaye, da jama'a cewa suyi watsi da labarin dake yawo a kafafen sada zumunta kan karin kudin makaranta."

"Shugabannin sun gana da daliban ranar Alhamis, 22 ga Afrilu, 2021 domin fadakar da su."

"Bayan haka, muna son sanar da cewa zamu yi karin kudin makaranta amma bamu sanar ba tukun."

KU KARANTA: Babu kasar da aka fi Najeriya yawan mutane marasa wutan lantarki, Bankin Duniya

Bamu kara kudin makaranta ba, amma zamu kara: Jami'ar jihar Kaduna KASU
Bamu kara kudin makaranta ba, amma zamu kara: Jami'ar jihar Kaduna KASU Credit: KASU
Asali: UGC

DUBA NAN: Wadanda suka daliban Kaduna sun bukaci N800m matsayin kudin fansa

Amma a tattaunawar Legit Hausa da wasu daliban jami'ar masu digiri na farko da kuma na biyu, sun bayyana cewa sabbin dalibai kadai suka ga kari yayinda suka nufi biyan kudin makaranta.

Hakazalika sun bayyana cewa muddin gwamnatin jihar tayi wannnan kari zasu bazama zanga-zanga saboda ko a yanzu da kyar wasu dalibai ke iya biya.

Aisha Dalha ta bayyana cewa: "Karin kudin makarantan da gaske ne amma ga sabbin dalibai. Sun fitar da takardar biya sai suka ga kudin yafi yadda ake biya."

"A baya a takaice yan tsangayar zane-zane (Art) bai wuci ka kashe N26,500, yan tsangayar Kimiya kuma bai wuce ka kashe N27,000 sai kuma kananan kudi kuma da ake biya. Amma gaba daya dai abi wuci mutum ya kashe N40,000 - N50,000 ba."

"Amma yanzu daliban tsangayar zane-zane (Art) yan asalin jihar Kaduna zasu biya N150,000, sannan baki su biya N170,000; yan tsangayar Kimiya yan asalin jihar su biya N170,000, baki su N221,000; masu karancin Likitanci kuma N300,000 yan asalin Kaduna, baki kuma N500,000."

Weedat mai digiri na biyu kuma tace: "Muna sauraro ko za'a kara ko ba za'a a kara ba amma na san zasuyi dole kuma zai fi na yan digirin farko."

"Dalibai na matukar bakin ciki gaskiya, saboda a haka ma mutane nawa ne sai sun kasa kudin sau biyu suke iya biya; su biya rabi zangon farko sannan su biya sauran kudin zango na biyu."

Asali: Legit.ng

Online view pixel