2023: Gwamnan PDP ya maidawa Bola Tinubu martani na cewa mutane za su sake zaben APC
- Seyi Makinde ya takali Bola Tinubu bayan ya fito ya ce za su cigaba da mulki
- Gwamnan jihar Oyo ya ce ba za a bar Jam’iyyar APC a kujera bayan 2023 ba
- Makinde ya ce dole a karbe mulki a hannun APC saboda halin da ake ciki yau
Gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde, ya maida wa jigon APC, Asiwaju Bola Tinubu, martani bayan ya fito ya ce jam’iyyarsa za ta cigaba da mulkin kasa.
Da yake magana a ranar Laraba, jaridar Daily Trust ta rahoto gwamna Seyi Makinde ya na cewa kwanakin jam’iyyar APC a mulki ya kusa zuwa karshe.
Mai girma gwamna Seyi Makinde ya ce mutanen kasar nan sun gaji da salon mulkin jam’iyyar APC.
KU KARANTA: Sukar Gwamnati ta jawowa tsohon ‘Dan Majalisar Katsina fushin DSS
Da yake jawabi wajen rantsar da sababbin shugabannin PDP na shiyyar Kudu maso yamma, Seyi Makinde ya zargi APC da mulkin da ya jagwagwala kasa.
An rantsar da shugabannin jam’iyyar hamayyar ne a gidan gwamnatin jihar Oyo da ke Ibadan.
Gwamna Makinde ya ce bai kamata a bar jam’iyyar APC ta cigaba da rike shugabanci bayan 2023 ba, a lokacin wa’adin shugaba Muhammadu Buhari zai kare.
Makinde yake cewa akwai bukatar shawo kan matsalolin rashin tsaro da matsin tattalin arziki da su ka dabaibaye ko ina karkashin gwamnatin APC mai-ci.
KU KARANTA: Dahiru Bauchi: Ba mu zabi Gwamnatin nan da nufin a rika kashe mu ba
“Dole mu nuna wa kasar nan baki daya cewa mun shirya karbe mulki a sama. Ina karanta jarida, sai na ji inda jagoran APC yake cewa za su yi mulki bayan 2023.”
“Ina so in ce wannan katuwar karya ce. Su fara jinmu daga zaben shugabannin Kudu maso yamma, kokarin ceto Najeriya ya kankama.” Inji gwamnan na Oyo.
Hakan na zuwa ne bayan an kammala zaben shugabannin PDP na shiyyar Yarbawa inda Bola Tinubu ya fito. A jihar Oyo ce kadai PDP ta ke da mulki a yankin.
A ranar Litinin jagoran jam’iyyar APC, Asiwaju Bola Tinubu ya samu damar gana wa da shugaba Muhammadu Buhari bayan an dauki tsawon lokacin ba su hadu ba.
Bola Tinubu ya ce APC za ta cigaba da mulki bayan 2023, kuma babu abin da ya shiga tsakaninsa da Buhari, sannan ya ce shugaban kasar ba zai yi turjiyar sauka ba.
Asali: Legit.ng