Matsalar tsaro: Lokacin tsige Buhari bai yi ba, Sanatan da yan bindiga suka addabi mazabarsa

Matsalar tsaro: Lokacin tsige Buhari bai yi ba, Sanatan da yan bindiga suka addabi mazabarsa

- Sanata Ali Ndume da Sanata Musa sun ce tsige Buhari ba zai tsinana komai ba

- A cewar Sanatocin, kawai matsalar tsaro suke son a kawar yanzu

- A bangare guda kuma dan majalisar wakilai, Dachung Bagos, ya ce da yiwuwan su fara shirin tsige Buhari

Sanata mai wakiltan mazabar Neja ta gabas, Mohammed Sani Musa, ya ce lokacin bukatar a tsige shugaba Muhammadu Buhari daga kujerarsa kan gazawarsa bai yi ba.

Yayin jawabi da manema labarai a Abuja ranar Talata, Musa ya ce tsige Buhari wani sabon rikici zai haifar kuma Najeriya ba ta bukatan hakan yanzu.

Musa ya bayyana hakan ne yayinda aka tambayesa shin meyasa Sanatoci basu shirin tsige Buhari sakamakon tabarbarewar lamarin tsaro a Najeriya, TheCable ta ruwaito.

"Duk mun san abinda tsige (shugaban kasa) ya kunsa. Wani sabon rikici ne. Shin me zai sa mu bukaci hakan yanzu? Abinda muke bukata shine mafita," cewar dan majalisar.

"Muna bukatan zaman lafiya ya dawo kasar nan. Zan fi son kowa ya mayar da hankali wajen magance matsalar tsaro."

"Duk abinda za muyi a kasar nan, ya kasance na magance tsaro. Babu zaman lafiya. Daga Kansila zuwa shugaban kasa, babu wanda ke bacci da idanuwansa a rufe."

"Ban son a ce don munada karfin tsige mu fara shirin haka yanzu."

KU KARANTA: Jerin kasashe 20 mafi rashin shugabancin kwarai a duniya, Rahoton Bincike

Matsalar tsaro: Lokacin tsige Buhari bai yi ba, Sanatan da yan bindiga suka addabi mazabarsa
Matsalar tsaro: Lokacin tsige Buhari bai yi ba, Sanatan da yan bindiga suka addabi mazabarsa Hoto: TheEmirateNG
Asali: Twitter

KU KARANTA: Babu cigaban da za'a samu a Najeriya muddin ana irin wannan cin hanci da rashawan, Ganduje

A bangare guda, Sanatan Musa yace kimanin ƙauyuka 42 ne ke ƙarƙashin ikon mayaƙan Boko Haram a jihar Neja.

Wannan na zuwa ne bayan gwamnan jihar Neja, Sani Bello, ya bayyana cewa yan ta'addan sun fara kafa tutocinsu a wasu ƙauyukan jihar, kamar yadda Dailytrust ta ruwaito.

Lokacin da yake magana a gaban takwarorinsa yan majalisar yau Talata, yayin da yake gabatar da kudiri a kan kashe-kashen da ake a ƙananan hukumomin Shiroro, Munya da kuma Rafi, jihar Neja.

Asali: Legit.ng

Online view pixel