Tsohon Jigon APC, Dr. Bugaje ya shiga hannun DSS bayan ya caccaki Gwamnatin Buhari

Tsohon Jigon APC, Dr. Bugaje ya shiga hannun DSS bayan ya caccaki Gwamnatin Buhari

- Dr. Usman Bugaje ya sha tambayoyi na yini guda a babban ofishin DSS a Abuja

- Tsohon ‘Dan Majalisar jihar Katsina ya shiga matsala bayan ya soki gwamnati

- Bugaje tsohon ‘Dan siyasa ne wanda ya yi aiki a Gwamnatin Olusegun Obasanjo

Jaridar Premium Times ta rahoto cewa a ranar Laraba, 28 ga watan Afrilu, 2021, jami’an DSS su ka tsare Usman Bugaje inda ya amsa tambayoyi.

Rahotanni sun tabbatar da cewa an yi ram da Dr. Usman Bugaje ne a game da wata hira da ya yi da gidan talabijin na AIT, inda ya soki gwamnati.

Wasu na-kusa da Bugaje sun ce ya kai kan shi hedikwatar DSS a garin Abuja ne da kimanin karfe 10:00 na safiyar jiya bayan an aika masa gayyata.

KU KARANTA: Farfesa Bugaje ya zama sabon Shugaban hukumar NBTE

Hukumar DSS ta tura wa tsohon ‘dan majalisar Jibiya/Kankia da goron gayyata ne bayan an yi hira da shi sau biyu a gidan talabijin na AIT a Abuja.

Bayan kimanin sa’o’i takwas ana yi masa tambayoyi, jami’an tsaron sun saki ‘dan siyasar. Da alama Bugaje ya bar ofishin DSS ne ana daf da za a sha ruwa.

“Usman Bugaje ya bayyana sau biyu a wani shiri da gidan talabijin na AIT ta shirya makonni biyu da su ka gabata, sai ya samu gayyata daga DSS cewa ana nemansa a ofishinsu domin ya yi karin haske kan wasu abubuwa da ya fada a shirin da aka yi.”

Majiyar ta kara da cewa: “A yau (Laraba kenan) da kimanin karfe 10:00 na sade, Dr. Bugaje ya hallara a ofishin DSS da ke Abuja, inda aka tsare shi.”

KU KARANTA: An bankado wadanda su ke wawurar kudi a Najeriya su na boyewa a ketare

Tsohon Jigon APC, Dr. Bugaje ya shiga hannun DSS bayan ya caccaki Gwamnatin Buhari
Dr. Usman Bugaje Hoto: katsinapost.com.ng
Asali: UGC

Jaridar ta ce sai kusan karfe 7:00 na yamma aka bada belin shugaban Arewa Research and Development Project (ARDP), sannan ya samu, ya tafi gida.

Bugaje wanda ya rike Sakatare a tsohuwar ACN, ya na cikin manyan APC, amma daga baya sai aka ji ya koma sukar gwamnatin Muhammadu Buhari.

Kafin yanzu Dr. Bugaje ya nemi takarar gwamnan jihar Katsina a 2007 da 2015, amma bai yi nasara ba. A 2016 ya ki karbar kujerar da Buhari ya ba shi.

A jiya an ji cewa babban malamin darikar Tijjaniyya, Sheikh Dahiru Bauchi ya gana da kiristoci, inda ya ce ana zaman firgici a halin yanzu a kasar nan.

Malamin ya yi kira ga gwamnati da ta yi maganin kashe-kashen da ake yi. Shehin ya bayyana wannan ne lokacin da ya zauna da kiristocin a Kaduna.

Asali: Legit.ng

Online view pixel