Kallabi tsakanin rawuna: Jajirtattun mata 'yan siyasa 5 a Najeriya

Kallabi tsakanin rawuna: Jajirtattun mata 'yan siyasa 5 a Najeriya

Akwai dalilai masu yawa da suka sa matan Najeriya basu shiga siyasa. Maza ne suka fi taka rawar gani a siyasar Najeriya. Dalilai kuwa da suka hada da al’ada da addini ne suke hana mata shiga taka rawar gani a siyasar Najeriya.

Najeriya ce ke da karancin mata a majalisar tarayya a fadin nahiyar Afirka. Mata takwas ne kacal a majalisar tarayyar Najeriya.

A zaben 2019, mata 2,970 ne suka fito neman kujeru daban-daban na siyasa. Hakan na nufin kashi 11.36 cikin dari na ‘yan takara a zaben mata ne.

Amma kuma, mata 64 ne suka samu nasarar hayewa kujerun mulki. Hakan na nuna cewa kashi 4.17 ne suka yi nasara. Amma kuma akwai wasu kalluba tsakanin rawuna da suka jajirce a zaben. Sun kasance madubin dubawa ga siyasar mata a Najeriya a shekarar 2019.

1. Natasha Akpoti

Ta fito takarar kujerar gwamnan jihar Kogi a karkashin inuwar jam’iyyar SDP. A yayin fafutukar neman samun jam’iyyar ta tsayar da ita, ta fuskanci kalubale mai tarin yawa. Duk da bata samu nasara ba, ta bayyana a ta uku. Jajircewarta da kokarinta yasa mutane da yawa ke mata kallon madubin dubawa a siyasar mata ta 2019.

DUBA WANNAN: Yanzu-yanzu: IG na 'yan sanda ya dakatar da gangamin taron da APC ta shirya a Edo

2. Oby Ezekweili

Wannan sanannen suna ne a Najeriya. Ta yi minista har sau biyu a Najeriya. A shekarar 2019, ta fito takarar kujerar shugabancin kasa karkashin jam’iyyar ACPN. Duk da daga baya ta janye, amma ta kafa tarihi mai matukar amfani a siyasar matan Najeriya

3. Hadiza Sabuwa Balarabe

Ita ce mataimakiyar gwamnan jihar Kaduna. Ba wai a suna kawai ta tsaya ba, tun farkon mulkin, ta kasance zakakura kuma jajirtacciyar mataimakiya ga gwamnan. Ita ce ta mika kasafin kudin shekarar 2020 ga majalisar jihar. Itace mace ta farko a Arewacin Najeriya da tayi hakan.

4. Abike Dabiri

Abike Kafayat Oluwatoyin Dabiri-Erewa tsohuwar ‘yar majalisar wakilan Najeriya ce. Itace shugaba ta farko ta ‘yan Najeriya da ke kasashen ketare. Itace mai bada shawara ga shugaban kasa a kan harkokin ketare. Babbar madubi ce ga mata kuma abar dubawa a siyasar 2019.

5. Abiodun Olujimi

Mace ce mai kamar maza kuma kallabi tsakanin rawuna. A halin yanzu tana wakiltar Ekiti ta Kudu a majalisar dattijai. Ta tashi tsaye wajen kalubalantar Sanata Adedayo Adeyeye bayan da INEC ta bayyana shi a matsayin wanda ya lashe zabe. Sun je har gaban kuliya inda nasara ta dawo mata da kujeru.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164