Abin da ya sa na rage zuwa Aso Rock – Tinubu ya yi magana kan ‘sabaninsa’ da Shugaba Buhari

Abin da ya sa na rage zuwa Aso Rock – Tinubu ya yi magana kan ‘sabaninsa’ da Shugaba Buhari

- Bola Tinubu ya ce babu abin da ya shiga tsakaninsa da Muhammadu Buhari

- Jigon APC ya na sa ran Jam’iyyarsu za ta cigaba da mulki a Najeriya a 2023

- Tsohon Gwamnan Legas ya ce Buhari ba zai rike shugabanci bayan 2023 ba

A ranar Litinin, 27 ga watan Afrilu, 2021, babban jagoran jam’iyyar APC, Asiwaju Bola Tinubu ya samu damar gana wa da shugaba Muhammadu Buhari.

An dauki tsawon lokaci biyun ba su zauna kamar yadda su ka saba ba, hakan ya sa ake rade-radin akwai rashin jituwa tsakanin shugaban kasar da Bola Tinubu.

Punch ta rahoto Asiwaju Bola Tinubu ya na cewa babu abin da ya shiga tsakaninsa da shugaban Najeriyar.

KU KARANTA: 'Yan Arewa zasu fi son Bola Tinubu ya karbi mulki a 2023

“Babu wani sabani da ya shiga dangantakar da ke tsakaninmu. Wanene ke duba alakarmu? Kafafen sada zumunta na zamani ne za su auna alakarmu?

Tinubu ya cigaba da cewa: “Ba na bukatar in addabe shi a gaban idanun kowa, haka ne? Yauwa, mu na da hanyoyi da yawa da za mu iya fuskantar abubuwa.”

Game da samun matsala da shugaban kasar, jigon na APC ya ce: “Babu wani abu irin hakan.”

Da aka nemi ya yi bayanin yadda dangatankarsa da Buhari ta ke, sai ya ce: "Akwai kusanci, mutunci da fadawa juna gaskiya ba tare da boye-boye ba.”

KU KARANTA: Fulani Buhari ya ke yi wa sharar fage - Ortom

Abin da ya sa na rage zuwa Aso Rock – Tinubu ya yi magana kan ‘sabaninsa’ da Buhari
Bola Tinubu
Asali: Facebook

Tsohon gwamnan na jihar Legas ya na ganin jam’iyyar APC za ta cigaba da rike mulki a 2023.

“Ba na so in yi hasashen wannan yanzu, ba na so in tabo wannan batu. Akwai alamu masu karfi da ke nuna za mu cigaba da mulki.” Inji babban ‘dan siyasar.

Game da wa’adin Muhammadu Buhari, Tinubu ya ce shugaban kasar ba zai kara sa’a guda a kan kujera da zarar lokacinsa ya yi ba, ya ce zai bi tsarin mulki.

A baya kun ji labarin rikicin cikin gidan da ya kunno kai a PDP, inda ake zargin Uche Secondus da majalisarsa sun cinye N10bn da aka tara daga saida fam.

Uwar jam'iyya ta yi martani, ta ce karya ne ake yi, domin ba a samu wadannan kudi ta hanyar saida wa ‘Yan takara fam a shekara hudu da su ka wuce ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng