Ba haka mu ka yi ba: Kowa zaman dar-dar yake yi saboda kashe-kashen da ake yi - Dahiru Bauchi

Ba haka mu ka yi ba: Kowa zaman dar-dar yake yi saboda kashe-kashen da ake yi - Dahiru Bauchi

- Sheikh Dahiru Bauchi ya ce ana zaman firgici a halin yanzu a kasar nan

- Bajimin Malamin ya yi kira ga gwamnati da ta yi maganin kashe-kashe

- Shehin ya bayyana wannan ne lokacin da ya zauna da kungiyar kiristoci

Shahararren malamin addinin musulunci, Sheikh Dahiru Usman Bauchi, ya fito, ya yi kira ga gwamnatin tarayya ta kawo karshen matsalar rashin tsaro.

Daily Trust ta ce dattijon malamin ya bayyana cewa babu wanda ya ke cikin zaman lafiya a kasar nan.

Jaridar ta rahoto Dahiru Usman Bauchi ya bukaci gwamnati ta sauke nauyin da ke kanta na kare jama’a daga ‘yan bindigan da su ke bi, su na kashe al’umma.

KU KARANTA: “Abubuwa sun cabe, dole mu mu nemi taimako - Sanata

Babban malamin ya yi wannan jawabi ne a lokacin da ya gana da tawagar wasu kiristoci a karkashin jagorancin tsohon Ministan tarayya, Salomon Dalung.

Solomon Dalung da Fasto Yohana Buru na cocin of Peace Revival and Reconciliation ne su ka kai wa shehin malamin ziyara a gidansa da ke garin Kaduna a jiya.

Shehin ya ce halin da ake ya isa a koka, ya ce lamarin ya zama abin takaici. Malamin ya ce ba ayi tunani abubuwa za su koma haka a karkashin gwamnatin nan ba.

“Abin da mu ke sa rai daga duka matakan gwamnati; tarayya, jihohi da kananan hukumomi shi ne su yi magana maganin matsalar nan, babu wanda ke zaune kalau.”

Kowa zaman dar-dar yake yi yanzu a Najeriya saboda kashe-kashen da ake yi inji Dahiru Bauchi
Dahiru Bauchi da Shugaba Buhari
Asali: UGC

KU KARANTA: Manyan su na yi wa Jami’an tsaro zagon-kasa inji Dattijon Arewa

“Ba ka cikin zaman lafiya a gida, ba ka zaune kalau a titi a waje, kuma gwamnati ba ta yi maganin wannan zaman dar-dar ba.” Inji fitaccen malamin addinin addinin.

“Ba mu zabe su saboda a shiga wannan hali ba, ba mu zabe su domin a rika saida mu kamar dabbobi ba, ko a rika yi mana kamar ba mu da gwamnati mai-ci.”

Dahiru Bauchi ya yi magana kan batun tsaro, ya yi kira ga Gwamnatin Buhari ta tashi-tsaye. Ya ce "Dole gwamnatin nan ta yi abin da ya dace, ta kare musulmai da kirista.”

Bauchi ya yi kira ga gwamnati ta saurari kukan da ake yi domin ba a iya zuwa gona. “Dole gwamnatin nan ta yi abin da ya dace, ta kare musulmai da kirista.”

Dazu ne ku ka ji cewa Malam Nasiru El-Rufai ya fadi abin da ya sa ya dawo daga rakiyar ba masu garkuwa da mutane kudin fansa kamar yadda aka saba yi a baya.

Gwamnan na jihar Kaduna ya yi raddi ga masu yada tsohon bidiyonsa da yake caccakar gwamnatin Goodluck Jonathan bayan an sace 'yan mata a Chibok

Asali: Legit.ng

Online view pixel