Sanatoci sun shiga dimuwa, sun ce da yiwuwan yan Boko Haram su kai hari Abuja

Sanatoci sun shiga dimuwa, sun ce da yiwuwan yan Boko Haram su kai hari Abuja

Sanatoci a ranar Talata sun bayyana tsoron cewa da yiwuwan yan ta'addan Boko Haram su kai hari birnin tarayya Abuja.

Sun bayyana hakan ne dubi ga irin hare-haren da ake kaiwa jihohin dake makwabtaka da ita.

A ranar Litinin, Gwamnan jihar Neja, Abubakar Sani Bello, ya ce yan Boko Haram sun kwace garuruwa 50 a jihar.

Bello ya ce nisan inda yan ta'addan ke zaune bai wuce tafiyar awanni 2 da Abuja ba.

Domin magance lamarin, Majalisar dokokin ta yanke shawaran tura wakilai wajen shugaba Buhari domin ganawa da shi. Amma ba su zabi ranar zuwa ba.

Yan majalisar sun yanke cewa shugabansu, Ahmad Lawan, ne zai jagoranci sauran shugabannin majalisar zuwa wajen Buhari, rahoton Guardian.

Hakazalika sun amince a sake sammatan sabbin hafsoshin tsaro don jin irin matakan da suke dauka wajen kawo karshen wannan lamari.

Sanatoci sun shiga dimuwa, sun ce da yiwuwan yan Boko Haram su kai hari Abuja
Sanatoci sun shiga dimuwa, sun ce da yiwuwan yan Boko Haram su kai hari Abuja Hoto: @NGRSenate
Asali: Facebook

Sanatan dake wakiltar mazaɓar Neja ta gabas a majalisar dattijai, Sanata Mohammed Sani Musa, yace kimanin ƙauyuka 42 ne ke ƙarƙashin ikon mayaƙan Boko Haram a jihar Neja.

Wannan na zuwa ne bayan gwamnan jihar Neja, Sani Bello, ya bayyana cewa yan ta'addan sun fara kafa tutocinsu a wasu ƙauyukan jihar, kamar yadda Dailytrust ta ruwaito.

Lokacin da yake magana a gaban takwarorinsa yan majalisar ranar Talata, yayin da yake gabatar da kudiri a kan kashe-kashen da ake a ƙananan hukumomin Shiroro, Munya da kuma Rafi, jihar Neja.

Sanator Musa yace sama da mutane 475 aka kashe a yankin da yake wakilta daga watan Janairu 2020 zuwa yanzun.

Asali: Legit.ng

Online view pixel