Sabon bincike: Najeriya ce kasa mafi rashin shugabannin kwarai ta 3 a duniya

Sabon bincike: Najeriya ce kasa mafi rashin shugabannin kwarai ta 3 a duniya

- Ya fara zama ruwan dare, wani sabon rahoto akan Najeriya maras dadin jiya ya bayyana

- Wata kungiyar shugabancin kwarai ta saki rahoto da ya nuna irin mummunan halin da Najeriya ke ciki

- A rahoto da kungiyar CGGI ta saki, an baiwa Najeriya matsayin kasa maras shugabannin kwarai ta uku a duniya

Wata kungiya mai zaman kanta a kasar Singapore, Chandler Good Government Index, CGGI ta bayyana Najeriya a matsayin kasa maras shugabannin kwarai ta uku a fadin duniya.

Rahoton ta baiwa Najeriya maki mai rauni wajen mulkin kwarai, inda Najeriya ta zo na 102 cikin kasashe 140 da maki 0.319.

Kasashen da Najeriya tafi shugabannin kwarai a cewa rahoton Zimbabwe da Venezuela ne kadai.

Rahoton da aka saki ranar 26 ga Afrilu, ya bayyana cewa an yi amfani da karfin iya yaki da rashawa wajen nuna irin nagartan shugabannin kasa.

Najeriya ta samu maki 0.44 a shugabanci; 0.45 a yaki da rashawa; 0.47 a hangen nesa; 0.41 a yin abinda da ya dace lokacin da ya dace; 0.4 a nazari.

CGGI ta yi bayanin cewa cutar Korona ta tona asirin raunin dokoki, shugabanni da ma'aikatun kasashen.

Diraktan CGGI, Wu Wei Neng, ya ce mulki na kwarai ne abinda zai iya kawo wa kasa nasara.

Sabon bincike: Najeriya ce kasa mafi rashin shugabannin kwarai ta 3 a duniya
Sabon bincike: Najeriya ce kasa mafi rashin shugabannin kwarai ta 3 a duniya Hoto: @ChandlerINST
Asali: Twitter

Asali: Legit.ng

Online view pixel