Rashin tsaro: Sanatan APC ya bukaci Buhari ya ajiye girman-kai, ya nemi taimakon kasashen waje
- Smart Adeyemi ya ce an shiga wani irin mummunar matsalar rashin tsaro
- Sanatan ya ajiye batun siyasa gefe guda, ya yi kira ga gwamnatinsu ta APC
- Adeyemi ya bukaci Muhammadu Buhari ya nemi taimakon kasashen waje
Sanata mai wakiltar mazabar Kogi ta yamma a majalisar dattawa, Smart Adeyemi, ya koka game da halin rashin tsaro da ake fama da shi a kasa.
A wani bidiyo da ya fito daga gidan talabijin na Channles TV, an ga Sanata Smart Adeyemi ya na jawabi, ya na koka wa kan bin da ya ke faru wa.
Za a ji Smart Adeyemi ya na cewa: “Wannan shi ne mafi munin tashin hankalin da mu ka shiga, kai, wannan ya fi lokacin yakin basasa muni.”
KU KARANTA: Bola Tinubu ya zauna da Shugaban kasa Buhari a Aso Villa
“Ba za mu cigaba da yi kamar za mu iya magance abubuwan da su ke faru wa a kasar mu ba.”
‘Dan majalisar ya ajiye siyasa, ya ce: “Kasa ta rikice, dole shugaban kasa ya tashi-tsaye, ya yi abin da ya dace. Ba za mu iya cigaba da yin shiru ba.”
“An kai yanayin da ba za mu iya barci da idanunmu a bude ba. ‘Ya ‘yanmu su na cikin kangi.” Sanatan ya ke fada a zauren majalisa a ranar Talata.
Adeyemi wanda ya canji Dino Melaye a majalisar dattawa ya ba gwamnatin tarayya shawarar abin da ya kamata ta yi domin ganin an samu tsaro.
KU KARANTA: Sanata Musa ba ya goyon bayan kiran a tunbuke Shugaban kasa
Fitaccen ‘dan siyasar ya yi kira ga Mai girma Muhammadu Buhari ya nemi taimako daga kasashen ketare, ya ce ya kamata a ajiye duk wata fankama a gefe.
Da yake bada gudumuwarsa a zaman da aka yi na jiya, an ji Sanata Remi Tinubu ta na neman zarginsa da zama ungulu da kan zabo a jam’iyyar APC.
Bisa dukkan alamu, Sanata mai wakiltar Legas ta tsakiya, Remi Tinubu ba ta ji dadin yadda ‘dan jam’iyyar na APC ya fito ya na irin wannan magana ba.
Yanzu nan mu ke ji cewa wasu 'yan sanda uku sun jikkata bayan 'yan bindiga sun budewa ayarin motocin Sanatan Edo Clifford Ordia, wuta a hanyar Okene.
Lamarin ya auku ne a ranar Litinin a hanyar Okene zuwa Lokoja a jihar Kogi bayan Sanatan ya baro garinsu a jihar Edo, ya na hanyar komawa birnin Abuja.
Asali: Legit.ng