Sai bango ya tsage: Wasu a Gwamnati su ke yi wa Jami’an tsaro zagon-kasa inji Dattijon Arewa
- Farfesa Khalifa Dikwa ya fadi inda ake samun cikas a yaki da ‘Yan Boko Haram
- Dattijon ya ce jami’an gwamnati ne su ka sa ba a iya ganin kokarin jami’an tsaro
- Dikwa ya bayyana cewa an hana ‘Yan Sanda da Sojoji kayan yakin da ake bukata
Daya daga cikin manyan kungiyar dattawan jihar Borno, Farfesa Khalifa Dikwa, ya yi magana a kan matsalar da ake samu a bangaren tsaro a halin yanzu.
Farfesa Khalifa Dikwa ya fito ya na ikirarin cewa akwai wasu miyagun mutane a cikin gwamnati da su ke da hannu a matsalar rashin tsaro da ake fama da ita.
A cewarsa, wasu daga cikin masu rike da madafan iko su na yi wa jami’an tsaro zagon-kasa ta hanyar hana su kayan aikin da su ke bukata a fagen fama.
KU KARANTA: Hare-hare 13 da ‘Yan bindiga da Boko Haram su ka kai a kwana 2
Dikwa ya ce wannan matsala ce ta sa har yau aka gagaro kawo karshen yakin Boko Haram da aka dauki shekara da shekaru ana yi a yankin Arewa maso gabas.
Farfesan ya yi wannan bayani ne a lokacin da ya bayyana a wani shiri na Politics Today a gidan talabijin na Channels TV a ranar Litinin, 27 ga watan Afrilu, 2021.
Dattijon ya ce gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari ta na da damar ta saye makamai daga wasu kasashen dabam idan wasu sun ki saida wa Najeriya kayan yaki.
Kamar yadda mu ka samu rahoto, Farfesa Dikwa ya jaddada muhimmancin sojoji su yi amfani da fasahar zamani domin su yi nasara a kan ‘yan ta’adda a Najeriya.
KU KARANTA: Za a ga canji a albashin ‘Yan siyasa da Malaman shari’a a 2021 - RMAFC
“Ya kamata shugaban kasa ya rika sanin abin da ke faruwa ta tauraron ‘dan adam. Tauraronmu zai iya nuna wa sojojinmu abin da ke wakana?” Dikwa ya tambaya,
Idan har dakarun Najeriya ba su da tauraron ‘dan adam na-kansu, ya kamata su nemi aron na wata kasa, Farfesan ya ce hakan ne zai sa ayi galaba a kan ‘yan ta’adda.
Dikwa ya ce ya kamata akwai jiragen saman da ke gani cikin dare amma dakarunmu duk ba su da wannan saboda ana yi wa jami’an sojoji da ‘yan sanda zagon-kasa.
A ranar Talata kun ji cewa matsalar rashin tsaro ta sa an bukaci ganin hafsoshin tsaro da hadimin Shugaban kasa, Babagana Monguno a majalisar wakilan tarayya.
Bayan haka majalisar tarayya ta fadawa gwamnatin tarayya ta sa dokar ta-baci a kan sha'anin tsaro domin a kare al’umma saboda ta'adin da ake fama da shi a yanzu.
Asali: Legit.ng