Gwamnatin Buhari ta fara aiki a kan taba albashin masu rike da mukaman ‘Yan siyasa

Gwamnatin Buhari ta fara aiki a kan taba albashin masu rike da mukaman ‘Yan siyasa

- RMAFC ta ce ana aiki domin a sake duba kudin da ake biyan ‘Yan siyasa

- Hukumar ta na kuma aiki a kan albashin Ma’aikatan da ke aikin shari’a

- Akwai yiwuwar ayi wa Jami’an gwamnatin kari ko ragi a karshen bana

Shugaban hukumar RMAFC mai alhakin tsaida albashin ma’aikata a Najeriya ya ce an fara zama a kan kudin da ake biyan ‘yan siyasa da malaman shari’a.

Jaridar The Cable ta ce shugaban RMAFC na kasa, Elias Mbam, ya bayyana wannan wajen wani biki da aka shirya a garin Amagu, karamar Ikwo, jihar Ebonyi.

A makon da ya gabata aka shirya bikin Ofala da na taya Mai martaba Ezeogo Aloh, Erima-Ogwudu III na kasar Amagu murnar cika shekara 30 a gadon sarauta.

KU KARANTA: PDP, Secondus sun cinye N10bn da aka tara tun daga 2017 - Afegbua

Rahoton ya bayyana cewa a wajen wannan taro, an ba Elias Mbam sarautar Aka Ekpuchi Onwa II.

Da yake magana da ‘yan jarida bayan an kammala taron, Elias Mbam ya bayyana cewa zuwa karshen shekara za a san matakin da aka dauka a kan albashin.

Sabon Aka Ekpuchi Onwan da aka nada ya ce kafin a ga canji a tsarin albashin ma’aikata da ‘yan siyasar, akwai jerin wasu abubuwa da gwamnati ta ke lura da su.

“Ana la’akari da karfin kudin kasa a kowane lokacin wajen yin wannan aiki, ana lura da tashin farashin kaya a kasuwa, karfin jimillar tattalin arziki, da sauransu.”

KU KARANTA: Za a kara yawan Sojoji, kawo sababbin dabaru da kaya - Minista

Gwamnatin Buhari ta fara aiki a kan taba albashin masu rike da mukaman ‘Yan siyasa
Shugaban RMAFC na kasa, Elias Mbam
Asali: UGC

Mbam ya ce: "Hukumar ta na ta-ka-tsan-tsan da cewa abubuwa da dama sun faru daga lokacin da aka yi canjin karshe zuwa yanzu. An fara wani shirin yin canjin.”

Har ya kammala jawabinsa, bai yi bayanin yadda karin zai kasance ba. Babu wanda ya san ko ana shirin yin karin albashi ne ko za a rage abin da ake biya ne a yanzu.

Shugaban hukumar ya ce: “An ci karfin wannan aiki, kuma nan da karshen 2021, za a san inda aka dosa. Idan ta kama ayi kari ne, za ayi, idan ta kama ayi ragi, za ayi.”

A jiya kun ji ana shirin ba kamfanonin raba wutar lantarkin da ake da su damar sama da kudin shan wuta. Amma da alama, wannan kari ba zai yi wa jama'a dadi ba.

NERC ta na magana da kamfanonin DisCos kan karin kudin shan wutar don haka mutane su fara jiran tsammanin wani sabon samfurin farashin lantarki daga DisCos.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng