‘Yan Sanda sun cafke ‘Yan bindiga, masu garkuwa da mutane 241 a jihar Katsina

‘Yan Sanda sun cafke ‘Yan bindiga, masu garkuwa da mutane 241 a jihar Katsina

- ‘Yan Sandan Katsina sun cafke wadanda ake zargi da laifin garkuwa da mutane

- Rundunar ‘Yan sandan ta yi ram da mutane sama da 240 a shekarar nan ta 2021

- Kakakin jami’an ya ce ana zargin su da yin fyade, satar mutane da kashe-kashe

Rundunar ‘yan sanda na reshen jihar Katsina sun ce sun yi ram da mutane 241 da ake zargi da aikata manyan laifuffuka a shekarar nan ta 2021.

Jami’an ‘yan sandan sun kama wadannan mutane ne bisa zargin yin fyade, garkuwa da mutane da kai wa Bayin Allah hari a watanni ukun farkon bana.

Jami’in da ke magana da yawun bakin ‘yan sanda na jihar Katsina, SP Gambo Isah ya bayyana wa jaridar Katsina Post wannan a cikin farkon makon nan.

KU KARANTA: An yi ram da wasu da ake zargin masu garkuwa da mutane ne a Zaria

Gambo Isah ya ce sun kama mutane 73 da ake zargin su da laifin yin garkuwa da mutane. An yi wannan kame ne daga farkon watan Junairu zuwa yanzu.

Da yake bayani, jami’in tsaron ya ce sun cafke mutum 55 a binciken da su ke yi a kan’yan bindigan da su ka addabi kauyuka da-dama na jihar Katsina.

Haka zalika jami’an ‘yan sandan sun kama mutumm 113 da ake bincikensu da laifin yin fyade.

Jihar Katsina ta na cikin inda ake fama da matsalar ‘yan bindiga da satar mutane. Masu wannan ta’adi su kan shiga gidaje a kauyuka ko makarantun boko.

KU KARANTA: Yan bindiga sun kona Kotun Tarayya a Ebonyi

‘Yan Sanda sun cafke ‘Yan bindiga, masu garkuwa da mutane 241 a jihar Katsina
Gwamnan jihar Katsina Aminu Masari
Asali: Twitter

Duka-duka, mutum 241 da ake zargi da aikata wadannan laifuffuka ne su ka shiga hannun ‘yan sanda kamar yadda kakakin jami’an tsaron ya yi bayani.

Ana sa ran cewa da zarar an kammala duk binciken da ya kamata, rundunar ‘yan sanda za ta gurfanar da wadannan mutane da ake tuhuma zuwa kotu.

A baya gwamnatin Aminu Bello Masari ta rika kokarin sulhu da ‘yan bindiga domin a samu zaman lafiya.

A makon nan ne aka ji cewa 'Yan bindiga sun saki bidiyon wata daga cikin daliban da suka sace daga kwalejin gandun dabbobi da ke Afaka a jihar Kaduna.

Wannan 'yar makaranta da aka sace ta na dauke da juna-biyu. An sace ta ne tare da sauran daliban wannan makaranta da aka yi garkuwa da su kwanaki

Asali: Legit.ng

Online view pixel