Babban labari: Gwamnatin Buhari ta kusa kammala maganar karawa 'Yan kasa farashin lantarki
- NERC ta na magana da kamfanonin DisCos kan karin kudin shan wutar lantaki
- Hukumar kula da wutan ba ta kammala tattauna wa da masu raba lantarkin ba
- Akwsi yiwuwar idan an karkare zaman da ake yi, farashin shan wuta zai tashi
Hukumar NERC mai kula da sha’anin wutar lantarki ta ce ta na kammala fito da sabon tsarin farashin shan wuta da kamfanoni za su yi amfani da shi.
NERC da ke da alhakin sa ido a kan sha’anin wutar lantarki a Najeriya ta bayyana wannan a ranar Litinin, 26 ga watan Afrilu, 2021, a shafinta na yanar gizo.
Jaridar Premium Times ta ce hukumar ta bayyana cewa an sake duba farashin shan wuta kamar yadda dokar wutar lantarki ta EPSRA na kasa ta yi tanadi.
KU KARANATA: Kamfanonin DisCos sun yi karin kudin wuta
A cewar hukumar ta NERC, farashin shan wuta ya na canza wa ne a duk lokacin da abubuwan da ake la’akari da su wajen shan lantarki su ka canza a kasar.
Kamar yadda sanarwar da aka fitar ta tabbatar, wannan mataki na sake duba kudin da ake saida wuta ya zama dole domin kamfanin DisCos su iya cin riba.
Har ila yau, NERC ta ce ta fara shirye-shirye domin a sake zama a kan tsarin Multi-Year Tariff Order (MYTO-2020) wanda aka saba duk bayan wata shida.
Za a yi amfani da kudin da ake kashewa wajen samar da wuta da raba lantarkin ga masu bukata kamar yadda EPSRA ta tsaida kafin a fito da sabon farashi.
KU KARANATA: Za a sha wuta kyauta na tsawon watanni 2 a Najeriya
Haka zalika hukumar za ta iya amfani da tashin farashin kaya, darajar kudin waje, farashin gas da adadin karfin wutan da ake da shi, kafin kara farashi.
“Hukumar ta zauna, ta tuntubi jama’a da masu ruwa-da-tsaki a kan maganar karin kudin shan wuta da DisCos su ka kawo domin inganta sha’anin wuta.”
Amma NERC ba ta iya kammala magana da kamfanonin wutan ba. Hukumar ta koma za ta saurari abin da mutane su ke fada kafin a tsaida magana."
Idan ana tsaida farashin shan wutar lantarki a kai-a kai ne kamfanin DisCos za su guje wa asara.
Kwanakin baya aka ji cewa Ministan harkokin wuta, Saleh Mamman, ya umarci NERC ta fadawa DisCos su dakatar da karin kudin wutan da su ka yi shirin yi.
Asali: Legit.ng