Ministan tsaro ya bayyana tanadin da Gwamnati ta ke yi a kan kashe-kashen da ya ki cinyewa

Ministan tsaro ya bayyana tanadin da Gwamnati ta ke yi a kan kashe-kashen da ya ki cinyewa

- Ministan tsaro na kasa ya ce za ayi wani abu a kan matsalar rashin tsaro

- Bashir Magashi ya bayyana cewa kwanan nan za a dauki wasu Sojoji aiki

- Gwamnatin Tarayya ta yi alkawarin kawo sababbin dabaru da makamai

Rundunar sojojin kasa za ta fara daukar mutane aiki domin a kara yawan dakarun Najeriya da nufin kawo karshen matsalar rashin tsaro da ake fama da shi.

Za a dauki mutane da-dama aiki daga cikin tulin matasan da su ke zaman kashe wando a kasar nan.

Ministan tsaro na kasa, Manjo-Janar Bashir Magashi (mai ritaya) ya bayyana wannan a lokacin da ya hadu da rundunar hadakar Operation Lafiya Dole.

KU KARANTA: Bayan hare-hare a Jami’a da Coci, ‘Yan bindiga sun dura Zaria cikin dare

Punch ta ce tawagar ta Operation Lafiya Dole da ta zauna da Janar Bashir Magashi a Borno ta na dauke da sojojin ruwa, sojojin sama da kuma sojojin kasa.

Ministan ya na tare da shugaban hafsun sojojin kasa, Laftana-Janar Ibrahim Attahiru da shugaban hafsun sojojin sama, Air Marshal Isiaka Amao.

Janar Bashir Magashi (mai ritaya) ya ce sun yi nazarin halin da ake ciki, kuma sun fitar da matakan da za a dauka domin ayi maganin duk wasu ‘yan ta’adda.

“Mun riga mun duba abubuwan da ake bukata, shiyasa yanzu mu ka zo nan domin mu tabbatar, mu ga yadda za mu yi maganin matsalolin nan.” Inji Magashi.

Ministan tsaro ya bayyana tanadin da Gwamnati ta ke yi a kan kashe-kashen da ya ki cinyewa
Ministan tsaro na kasa, Janar Bashir Magashi
Asali: Twitter

KU KARANTA: ICPC ta yi nasarar karbe N1.1bn, gidaje 29 daga barayi a 2021

Magashi yake cewa su na kokarin ganin yakin da ake yi da ‘yan ta’adda ya zo karshe ta yadda dakarun Najeriya da su ka yi fice a Duniya za su tashi da nasara.

“Kwanan nan za mu fara daukar sojoji da manyan jami’ai domin mu inganta adadin dakarunmu da ke aiki”

Ministan ya ce: “Za mu kawo sababbin kayan aiki, sababbin dabaru, ina so dukkanku ku amfana da su, saboda aikinku ya kara yin kyau, ku yi nasara a fagen fama.”

A jiya ne wasu rahotanni daga ƙaramar hukumar Geidam na jihar Yobe su ka tabbatar da cewa mayaƙan Boko Haram sun fara kafa tutocin su a wannan garin.

Wannan na zuwa ne bayan kwanaki biyu da wasu ;yan ta'addan suka kai hari yankin ƙaramar hukumar Geidam, inda nan ne mahaifar tsohon gwamnan jihar Yobe.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng