Obasanjo ya jinjinawa Tambuwal, ya fadi inda Gwamnan ya sha ban-ban da sauran 'Yan siyasa

Obasanjo ya jinjinawa Tambuwal, ya fadi inda Gwamnan ya sha ban-ban da sauran 'Yan siyasa

- Tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo ya ziyarci jihar Sokoto

- Olusegun Obasanjo ya yabi aikin da Gwamnatin Tambuwal ta ke yi

- Obasanjo ya jinjinawa Gwamnan, ya ce ya yi zarra a takwarorinsa

Tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo, ya bayyana, Rt. Hon. Aminu Waziri Tambuwal, a matsayin shugaba mai hangen nesa da kawo gyara a al’umma.

Jaridar The Nation ta ce tsohon shugaban na Najeriya ya bayyana haka ne a lokacin da ya kafa tubulin ginin wata katafariyar gadar sama da za ayi garin Sokoto.

Za a kashe Naira biliyan 3.4 kafin a kammala aikin wannan babbar gada sama mai hanyoyi tara.

KU KARANTA: Majalisar Dattawa ta yabawa aikin a-yaba da ICPC ta ke yi

Cif Olusegun Obasanjo ya yabi aikin da Mai girma Aminu Tambuwal yake yi musamman a harkar gina abubuwan more-rayuwa da inganta rayuwar marasa hali.

“Duk da matsalar da ake ciki yanzu na matsin tattalin arziki da rashin tsaro, ga tasirin annobar COVID-19, duk da karancin kudin-shiga, Tambuwal aiki ya ke yi.”

Ya ce: “Ina nan a baka ta cewa gwamna ne wanda ya ke aiki a jiharsa, ba a jiharsa kurum ba, daukacin Arewa maso yamma, musamman a bangaren kawo tsaro.”

“Ya na yin kokarin gaske, har a cikin abokan aikinsa da jam’iyyarsa, ya yi fice.” Inji Obasanjo.

KU KARANTA: Sanusi ya yi magana a kan mutuwar Mai babban daki, ya ce an yi rashi

Tsohon Shugaban kasa Obasanjo ya jinjinawa Tambuwal, ya ce Gwamnan ya yi fice a PDP
Gwamnan Sokoto. Aminu Waziri Tambuwal
Asali: UGC

Obasanjo wanda ya yi mulki na tsawon shekar takwas a baya, ya hada da addu'a: “Ina addu’a Ubangiji ya ba shi kwarin-gwiwa da karfin yin abin da ya zarce wannan.”

A cewar Obasanjo, gwamnan na Sokoto ‘dan siyasa ne wanda yake kaunar jama’a daga ko ina. Obasanjo ya ce ya ji dadin gane wa kansa irin aikin da gwamnan yake yi.

Obasanjo yake cewa: “A tsawon sa’o’i 24 da na yi a birnin nan, naga gadojin da ake gina wa, kuma na samu damar kaddamar da daya aikin wani daga cikin wadannan gadoji.”

A kwanan baya kun ji cewa Duniya ta yabi salon mulkin Yahaya Bello musamman ta harkar bunkasa ilmi a jihar Kogi da yadda yake dama wa mata a Gwamnatinsa.

Jami’ar Amurkar ta European American University, Commonwealth of Dominican Republic ta ce wannan shi ne dalilin da ya sa ta zabi Gwamnan Kogi, za ta ba shi PhD.

Asali: Legit.ng

Online view pixel