Za a sha wuta kyauta na tsawon wata 2 a Najeriya, FG da Discos sun amince

Za a sha wuta kyauta na tsawon wata 2 a Najeriya, FG da Discos sun amince

Hadakar kamfanonin rarraba hasken wutar lantar na kasa (DisCos) sun sanar da cewa sun ji kiran gwamnatin tarayya a kan bawa jama'a wutar lantarki kyauta har na tsawon wata biyu don rage musu radadin matsin dokokin killacewa saboda annobar cutar covid-19.

A jawabin da darekta a kungiyar masu rarraba hasken wutar lantarki (ANED), Barista Sunday Oduntan, ya fitar ya sanar da manema labarai a ranar Laraba cewa sun yanke wannan shawara ne don sanin halin kalubalen tattalin arziki da jama'a ke fuskanta a wannan lokaci.

Oduntan, wanda shine kakakin DisCos, ya ce, "mun ji kiran gwamnatin tarayya a kan bawa jama'a wutar lantarki ta tsawon watanni biyu kyauta dmina saukaka musu rayuwa a yayin da aka hana walwala da zirga-zirga. Bayanai dalla-dalla a kan tsarin kaddamar shirin na nan tafe."

DisCos sun bayyana aniyarsu ta tabbatar da samar da wutar lantarki ba yankewa yayin dokar hana walwala da ma bayan janyeta. Kazalika, sun shawarci jama'a su zauna a gida tare kiyaye dukkan matakan kare kai daga kamuwa ko yada cutar covid-19.

Za a sha wuta kyauta na tsawon wata 2 a Najeriya, FG da Discos sun amince
Za a sha wuta kyauta na tsawon wata 2 a Najeriya, FG da Discos sun amince
Asali: UGC

A cikin daya daga cikin labaran Legit.ng, ta wallafa cewa akwai yuwuwar annobar coronavirus din ta lalata zamantakewa, musamman a tsakanin ma'aurata.

A saboda haka ne gwamnatin kasar Dubai ta dakatar da aure da saki har sai yadda hali yayi don gujewa taron da zai iya zama sanadin yaduwar cutar coronavirus.

DUBA WANNAN: Covid-19: Likitocin kasar China 15 sun iso Najeriya (Bidiyo)

Sashen shari'a na kasar Dubai ne ya sanar da wannan hukuncin a ranar Laraba don samar da mafita wajen dakile yaduwar muguwar annobar. Hakan kuwa na iya bada gudumawa wajen assasa dokar hana walwala a kasar.

Jastis Khaled al-Hawsni na kotun iyali ya kara da cewa, sashin shari'ar ya bayyana cewa jama'a masu tarin yawa a kasar sun cike sharuddan aure ta yanar gizo.

Don haka ba za a hana su gudanar da daurin aure ba, amma kada su hada liyafa "koda kuwa a cikin gida ne."

Kasar UAE na da mutane 2,000 da suka kamu da muguwar cutar covid-19, kuma mutane 12 ne suka rasa rayukansu, kamar yadda gidan talabijin din Channels ya bayyana.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel