Hukumar ICPC ta karbowa Gwamnatin Buhari fiye da Naira Biliyan a cikin watanni 3

Hukumar ICPC ta karbowa Gwamnatin Buhari fiye da Naira Biliyan a cikin watanni 3

- Shugaban hukumar ICPC ya bayyana irin kokarin da jami’ansa su ke yi

- Farfesa Bolaji Owasanoye ya ce sun karbowa gwamnati Naira Biliyan 1

- Bayan haka, ICPC ta karbe gidaje da wasu dukiyoyi daga hannun barayi

Rahotanni sun tabbatar mana da cewa hukumar nan ta ICPC mai yaki da cin hanci da rashawa ta bayyana adadin kudin da ta karbe a farkon shekarar nan.

Shugaban hukumar ta kasa, Farfesa Bolaji Owasanoye, ya ce tsakanin watan Junairu zuwa Maris na shekarar bana, sun karbo wa gwamnati Naira biliyan 1.1.

Bolaji Owasanoye ya yi wannan bayani ne a makon da ya gabata, a sa’ilin da ya sadu da ‘yan kwamitin yaki da cin hanci da rashawa na majalisar datttawa.

KU KARANTA: Buhari ya ba Isa Pantami kariya, ya nuna ba zai tsige Ministan ba

‘Yan kwamitin yaki da cin hanci da rashawa a karkashin shugabansu, Suleiman Abdu Kwari sun ziyarci shugaban hukumar ta ICPC ne a ofishinsa da ke Abuja.

Farfesa Bolaji Owasanoye ya shaida wa Sanata Suleiman Abdu Kwari da ‘yan tawagarsa cewa sun sa an maida wa gwamnatin tarayya N418m da fam Dala $1.5m.

A cewar Bolaji Owasanoye, ICPC ta yi wannan kokari ne a watanni ukun farkon shekarar nan.

Har ila yau, Bolaji Owasanoye ya ce sun yi nasarar karbe filaye biyar, kasuwanni 13, da gine-gine 29 mota daya da kuma makamai biyar a tsakanin wannan lokaci.

KU KARANTA: Matsayar APC na rashin goyon bayan a kara kudin fetur ya jawo hayaniya

Hukumar ICPC ta karbowa Gwamnatin Buhari fiye da Naira Biliyan a cikin watanni 3
Shugaban hukumar ICPC, Bolaji Owasanoye
Asali: UGC

Hukumar ICPC ta ce ta shigar da kara 73 a kotu a shekarar 2020, amma daga farkon shekarar nan ta 2021 zuwa watan Maris, kara 11 ta iya kai wa gaban kotu.

Kamar yadda Owasanoye ya bayyana, ICPC ta samu nasarar daure mutane 26 da aka samu da laifi a shekarar bara, a shekarar bana kuwa, an kama mutane hudu.

Da yake jawabi, Sanata Kwari ya yaba da irin nasarorin da ICPC ta samu zuwa yanzu, ya tabbatar da cewa majalisar dattawa za ta ba ta goyon bayan da ta ke bukata.

A jiya kun samu labari cewa Malam Kabiru Dakata, wani ‘dan gwagwarmayan ya ce wasu mutane su na binsa tun da ya tado batun ‘Gandollars’ a wata hira.

Wanannan Matashi ya zama mutum na uku da yake zargin Gwamnatin Kano ta na farautarsa. Kafinsa akwai Jafar Jafar da wata Sa'ida Bugaje da te ke Kaduna.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng