Jose Mourinho zai tashi da Naira Biliyan 8 a asusunsa duk da Tottenham ta sallame shi

Jose Mourinho zai tashi da Naira Biliyan 8 a asusunsa duk da Tottenham ta sallame shi

- A farkon makon nan aka kori Jose Mourinho daga kungiyar Tottenham

- Daniel Levy zai biya kocin tulin kudin da ya haura Naira Biliyan takwas

- Mourinho ya tashi da fiye da $100m bayan an kori shi a kungiyoyi hudu

Jose Mourinho, wanda aka sallama daga aiki a matsayin mai horas da ‘yan wasan kungiyar Tottenham zai tashi da kudin da ya kai fam miliyan £20.

Tottenham ta na biyan Jose Mourinho albashin kusan Dala miliyan 20 duk shekara kafin kungiyar ta katse kwantiraginsa bayan watanni 17 kacal.

Rahotanni sun bayyana cewa yarjejeniyar da aka yi shi ne za a cigaba da biyan Mourinho kudin da aka saba ba shi a duk shekara, har sai ya samu wani aiki.

KU KARANTA: Koci 4 da za su iya maye gurbin Mourinho a Tottenham

Ya kamata Mourinho ya yi shekaru hudu a Tottenham domin kwantiragin da ya rattaba hannu a kai zai kare ne a 2023, amma karshe ba a cika alkawarin ba.

Idan wannan rahoto ya tabbata gaskiya ne, a darajar kudin mu na gida, abin da ake maganar za a biya Kocin mai shekara 58 sun haura Naira biliyan takwas.

Kafin zuwansa Tottenham, Mourinho ya yi aiki a kasashe hudu a Turai, ya horas da Porto, Chelsea, Inter Milan, Real Madrid da kuma Manchester United.

Da aka yi lissafi, Jose Mourinho ya samu kimanin $100m (kimanin Naira biliyan 40) a sakamakon korarsa da aka yi a Chelsea, Manchester United da Real Madrid.

KU KARANTA: Mourinho zai canji Pochettino - Tottenham

Jose Mourinho zai tashi da Naira Biliyan 8 a asusunsa duk da Tottenham ta sallame shi
Jose Mourinho
Asali: Twitter

Amma bisa dukkan alamu wannan karo za a dauki lokacin kafin Jose Mourinho ya sake samun wani aikin ganin yadda abubuwa su ka tabarbare masa a Landan.

Mourinho ya bar Tottenham da mafi munin sakamako tun da ya yi suna a Duniya. A cikin wasanni 86, ya ci 44, ya rasa 23, sannan ya yi canjaras a ragowar 19.

A karkashin Mourinho, Tottenham ta gaza tabuka abin kirki a Turai. Sannan a bana an yi waje da shi a gasar kofin FA, kuma kungiyar ta kai ta bakwai a Firimiya.

A jiya kun ji cewa Jose Mourinho ya kafa bakin tarihin zama Kocin da kungiyoyi 3 su ka tsige a kasar Ingila. Wannan ya sa wasu ke ganin ta kare wa babban kocin.

Bayan Jose Mourinho, Tottenham ta sallami duka masu taya shi horas da ‘yan kwallon ta, Joao Sacramento, Nuno Santos, Carlos Lalin da kuma Giovanni Cerra.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng