Yabon gwani: Za a karrama Gwamna Bello da Ministan Buhari da lambar yabo a kasar waje

Yabon gwani: Za a karrama Gwamna Bello da Ministan Buhari da lambar yabo a kasar waje

- Wata Jami’a a Dominican Republic za ta ba Yahaya Bello kyautar digir-digir

- Wannan jami’a ta ce Gwamnan jihar Kogi ya cancanci ya samu lambar yabo

- Haka zalika jami’ar za ta karrama karamin Ministan harkokin wuta na kasa

Majalisar da ke kula da harkokin jami’ar babbar jami’ar Amurkar na kasar Dominican, za ta karrama wasu ‘yan siyasa da su ka yi fice daga Najeriya.

Jaridar Daily Trust ta fitar da rahoto cewa jami’ar European American University, Commonwealth of Dominican Republic za ta ba ‘yan siyasar lambar yabo.

Daga cikin wadanda za a karrama har da wani gwamna daga jihar Arewa da Ministan tarayya.

KU KARANTA: Hester Ford, Matar da ake tunanin ta girmi kowa a Amurka ta mutu

Kamar yadda jawabin da jami’ar ta fitar ta bakin Dr. Josephine Egbuta, masu karbar lambar sun nuna kokari wajen shugabanci na gari da taimakon al’umma.

Wadannan mutanen da za a ba lambar yabo sun hada da mai girma gwamnan jihar Kogi, Alhaji Adoza Yahaya Bello. Gwamnan zai samu digirin girmama wa.

Jami’ar za ta ba Adoza Yahaya Bello kyautar digiri na uku a fannin tattalin kudi da ilmin akawu.

Josephine Egbuta ta ce sun zabi gwamnan Kogi ne saboda samun labarin kokarin da yake yi a mulki musamman wajen harkar ilmi da tafiya da mata a siyasa.

KU KARANTA: Kwastam sun karbe buhunan shinkafa 37,000 a 2021

Yabon gwani: Za a karrama Gwamna Bello da Ministan Buhari da lambar yabo a kasar waje
Gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello
Asali: UGC

Jami’ar makarantar ta European American University, Commonwealth ta kuma bayyana cewa za su bada irin wannan kyautan digiri ga Mr. Goddy Jeddy Agba.

Goddy Jeddy Agba shi ne ke rike da kujerar karamin Ministan wuta. Misis Josephine Egbuta ta ce tun ba yau ba, ya kamata ace an ba Agba wannan lambar yabo.

Gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai ya ce duka Gwamnonin jihohi sun yi ittifaki a kan murkushe ‘Yan bindigan da su ka fake a jeji, su na yin aika-aika.

Malam Nasir El-Rufai ya bayyana haka ne a wajen wani taro da aka shirya a Abuja a tsakiyar makon nan, inda aka tattauna game da sha’anin karatun boko.

Asali: Legit.ng

Online view pixel