Tsohon Sarki Sanusi ya aiko sakon ta’aziyyar Mahaifiyar Sarakunan Kano daga kasar waje

Tsohon Sarki Sanusi ya aiko sakon ta’aziyyar Mahaifiyar Sarakunan Kano daga kasar waje

- Muhammadu Sanusi II ya yi magana a kan mutuwar Maryam Bayero

- Sanusi II ya aiko da sakon ta’aziyyarsa, ya na cewa an yi babban rashi

- Tsohon Sarkin Kano ya yi wa Mai babban dakin addu’o’i ne a karatunsa

Legi.ng Hausa ta samu labari cewa tsohon Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II ya aiko sakon ta’aziyyarsa na mutuwar Hajiya Maryam Ado Bayero.

A wani bidiyo da yake yawo a dandalin sada zumunta na zamani, Malam Muhammadu Sanusi II ya yi magana game da babban rashin da aka yi a Kano.

Da yake jawabi a jiya, Sanusi II ya ce: “Yau mun tashi da rasuwar mahaifiyarmu, Maryam Bade (Ado Bayero), uwargidar marigayi Sarki Ado Bayero.”

KU KARANTA: Sanusi Lamido, zai koma makaranta bayan ya rasa sarauta

Mai martaban ya cigaba da cewa: “Ta rasu a kasar Masar, mu na mika ta’aziyya ga daukacin al’umma.”

A wannan bidiyo da wani mai suna Kwankwason Twitter ya wallafa a shafinsa, Muhammadu Sanusi II ya yi wa marigayiyar addu’a tare da sauran jama’a.

“Allah ya sa ta huta, Allah ya sa ciwon da ta yi ya zama kaffara.” Sanusi ya ke cewa za ayi rashin mahaifiyar magajinsa da kuma Sarki Nasiru Ado Bayero.

Malam Sanusi II wanda ya bar karagar mulki a bara ya sa an yi wa marigayiyar salatin Annabi SAW kafa 10 da karatun suratul Ikhlas domin ta samu ceto.

KU KARANTA: Mahaifiyar sarkin Kano, Maryam Bayero, ta rasu

Tsohon Sarki Sanusi ya aiko sakon ta’aziyyar Mahaifiyar Sarakunan Kano daga kasar waje
Tsohon Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II
Asali: UGC

Mai martaban wanda ya rike kujerar gwamnan babban bankin Najeriya na CBN ya kira Hajiya Maryam Ado Bayero wanda ta rasu a ranar Juma’ar nan.

A karshe bayan tsohon Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II ya yi wa Mai babban daki addu’a, ya kuma yi addu’a ga sauran wadanda su ka riga mu cika wa.

Sarauniya Maryam Ado Bayero ta bar Duniya ne bayan kusan shekaru bakwai da mutuwar Ado Bayero.

Kwanaki baya Sarki Alhaji Aminu Ado-Bayero, ya ziyarci Sarkin kasar Oyo, ya yaba da basirar Alaafin na kasar Oyo, Oba Lamidi Adeyemi wajen rike kasarsa.

Mai martaba Sarkin Kano, Alhaji Aminu Ado-Bayero ya bayyana cewa a shirya yake da ya dauki darasi da shawarar dattijon Basaraken mai shekara 82.

Asali: Legit.ng

Online view pixel